Korar Alkalin-Alkalai: Wani babban masanin shari'a ya goyi bayan shugaba Buhari

Korar Alkalin-Alkalai: Wani babban masanin shari'a ya goyi bayan shugaba Buhari

Daya daga cikin manyan masana harkokin shari'a kuma mai sharhi akan lamurran yau da kullum, Farfesa Itse Sagay (SAN) ya bayyana matakin dakatarwa da shugaba Buhari ya dauka kan Alkalin-Alkalin Maishari'a Walter Onnoghen a matsayin wanda ya kamata kuma ya dace.

Farfesa Sagay ya bayyana cewa shugaba Buhari yayi abunda ya kamata a shari'ance domin ya yi biyayya ga umurnin kotun tabbatar da da'ar ma'aikata da ta bukaci ya dakatar da alkalin alkalan.

Korar Alkalin-Alkalai: Wani babban masanin shari'a ya goyi bayan shugaba Buhari

Korar Alkalin-Alkalai: Wani babban masanin shari'a ya goyi bayan shugaba Buhari
Source: UGC

KU KARANTA: An gano sabuwar hanyar magudi da Atiku ya shirya

Legit.ng Hausa ta samu cewa Farfesan na shari'a ya kuma kara da cewa duk da kundin tsarin mulki bai ba shugaban kasa damar cire Alkalin-Alkalai ba, amma ta bashi damar dakatar da shi har sai 'yan majalisar dattawa sun amince ko kuma akasin hakan.

Ita ma dai kungiyar dake rajin kare hakkokan mabiya addinin musulunci a tarayyar Najeriya Muslim Rights Concern (MURIC) a turance ta bayyana dakatarwar da shugaba Buhari yayiwa Alkalin Alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen a matsayin abun da ya kamata kuma sadda ya kamata.

Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola shine ya bayyana hakan a ranar Juma'a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar jim kadan bayan da shugaban kasar ya rantsar da sabon Alkalin Alkalan a fadar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel