Bayan korarsa daga mukamin CJN: An gano dalilin Onnoghen na dakatar da taron NJC

Bayan korarsa daga mukamin CJN: An gano dalilin Onnoghen na dakatar da taron NJC

Walter Onnoghen, tsohon alkalin alkalai na kasa (CJN), ya dakatar da taron majalisar zartaswa ta shari'ar kasa (NJC) awanni 11 kafin taron ba tare da bayyana wani dalili ba. Sai dai, jaridar SaharaReporters yanzu ta gano dalilin da ya sa ya dauki wannan matakin, wanda baya rasa nasaba da tsoron kar majalisar ta tsige shi.

Majalisar NJC ta gudanar da taronta na 87 a ranar 3 ga watan Oktoba, karkashin jagorancin Onnoghen. A karshe taron, an kawo bukatar nada babban alkali na kotun koli, manyan masu shari'a, da kuma sauran wasu masu shari'ar na manyan kotunan jiha da kuma alkali a kowacce kotun shari'a da kotun daukaka kara da kotun al'adu ta daukaka kara. An shirya gudanar da taron majalisar na 88 a ranar Talata, 15 ga watan Janairu, 2019, wanda Onnoghen ya dage.

Sai dai bayan wasu 'yan kwanaki, hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta maka alkalin alkalan a kotun da'ar ma'aikata (CCT) kan zarginsa da kin bayyana kadarorin da ya mallaka. Cike da tsoron cewa majalisar NJC zata dakatar da shi saboda wannan dalilin, Onnoghen, duk da sanin cewa tuni mambobin majalisar suka isa Abuja, ya dakatar da taron har sai baba-ta-gani.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya nada Ibrahim Tanko Muhammed mukaddashi

Bayan korarsa daga mukamin CJN: An gano dalilin Onnoghen na dakatar da taron NJC

Bayan korarsa daga mukamin CJN: An gano dalilin Onnoghen na dakatar da taron NJC
Source: UGC

Wata majiya da ke da masaniya akan lamarin, ta shaidawa SaharaReporters cewa Onnoghen ya dauki wannan matakin ne bayan da lauyoyinsa suka bashi shawara, la'akari da yunkurin da majalisar ke yi na daukar mataki akansa.

Sau biyu dai Onnoghen na kin halartar zaman kotun CCT. A hannu daya kuwa, babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja da kuma kotun masana'antu, sune suka dakatar da kotun CCT daga ci gaba da sauraron karar.

Sai dai a jiya Juma'a, shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi. Legit.ng ta samu wannan rahoto ne daga bakin hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafofin sada zumunta. Bashir Ahmad inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da shugaban alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, kuma ya nada Mr Ibrahi Tanko Muhammed matsayin mukaddashin Alkalin alkalai."

"Shugaba Buhari ya sallameshi ne bisa ga umurnin kotun hukunta ma'aikatan gwamnati CCT"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel