Zaben fidda gwani: Na yafewa APC - Gwamna Yari

Zaben fidda gwani: Na yafewa APC - Gwamna Yari

- Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ce ya yafewa dukkan 'yan jam'iyyar APC da suka musguna masa game da batun gudanar da zaben fidda gwani a jihar

- Gwamnan ya yi wannan maganar ne bayan wata kotun jihar Zamfara ta yanke hukunci unda ta tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwani a jihar

- Wannan na zuwa ne a lokacin da wata kotu a Abuja ta yanke hukuncin cewa INEC tana da ikon kin karbar sunayen 'yan takarar daga Zamfara saboda rashin gudanar da zaben fidda gwanin da mika suyanen a kan lokaci

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce ya yafewa dukkan 'ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bisa rashin adalcin da suka yi masa a kan zaben fidda gwani da akayi a jihar a 2018.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock da ke Abuja. Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC na jihar Zamfara, Mukhtar Idris ne ya yiwa gwamnan rakiya.

Na yafewa jam'iyyar APC - Gwamna Yari

Na yafewa jam'iyyar APC - Gwamna Yari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben fidda gwani: Na yafewa APC - Gwamna Yari

Yari ya ce hukuncin da kotu ta yanke a kan zaben ya wanke shi daga zargi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

A ranar Juma'a 25 ga watan Janairu ne wata babban kotun jiha na 3 da ke zamanta a Gusau ta yanke hukuncin amincewa da zaben fidda gwamni da jam'iyyar APC na jihar Zamfara tayi a baya.

A ranar 11 ga watan Oktoban 2018, jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ya shigar da kara kotu inda ya nemi a tilastawa uwar jam'iyyar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC amincewa da zaben fidda gwani da jam'iyyar ta gudanar a ranar 7 ga watan Oktoban 2018.

A baya, hedkwatan jam'iyyar na kasa ta ce ba a gudanar da zaben fidda gwani a jihar na Zamfara ba.

A yayin da ya ke magana bayan gana da shugaban kasar a Abuja, Yari ya ce: "Sashi na 87, 1 zuwa 1 na Dokar Zabe ya bayyana matakin da za a dauka karara amma an tauye mana hakokin mu da dama, sai dai kamar yadda na ce a baya, mun yafewa kowa kuma za mu cigaba.

"Idan ka tuna, daga Oktoban 2018, muna ta kaiwa da komowa da INEC a kan batun gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara.

"Yau, Allah ya bamu nasara, Kotu ta tabbatar cewa an gudanar da zaben fidda gwani a jihar Zamafara saboda hujojin da aka gabatar mata."

Gwamna Yari cigaba da cewa, "Hukumar zabe na jihar REC ta zagaya ta duba yadda ake gudanar da zaben fidda gwani kamar yadda doka ta tanada amma hedkwatan INEC na Abuja ba ta jira an tura mata rahoto ba sai ta bayyana cewa ba ayi zaben fidda gwani a Zamfara ba.

"Muna da shaidar zaben na ainihi kuma mun gabatar da shi a kotu kuma ina kyautata zaton shine ya sanya kotun ta bamu nasara a kotun."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel