Dakatar da Onnoghen: Jam'iyyar PDP ta dage kamfen din Atiku

Dakatar da Onnoghen: Jam'iyyar PDP ta dage kamfen din Atiku

Kungiyar yakin neman dan takarar shugabancin kasa na Jam'iyyar Peoples Democratic PDP ta dage kamfen din ta domin nuna kin amincewa da dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a jiya Juma'a.

Wannan dagewar ya sa jam'iyyar ba za ta gudanar da yakin neman zaben ta a jihar Benue ba a ranar Asabar kamar yadda ta shirya a baya.

An gano cewa jam'iyyar ta yanke shawarar dage yakin neman zaben ne saboda nuna "goyon bayanta ga fannin shari'a na Najeriya."

Dakatar da Onnoghen: Jam'iyyar PDP ta dage kamfen din Atiku

Dakatar da Onnoghen: Jam'iyyar PDP ta dage kamfen din Atiku
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen Walter Nkanu Samuel Onnoghen a matsayin aikin kama-karya mai muni.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a 25 ga watan Janairu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da Justice Onnoghen ne a dakin taron Majalisa da ke Fadar Aso Rock a ranar Juma'a.

Shugaban kasar ya nada Justice Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukadashin Alkalin Alkalan na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel