Ashe $1m aka sacewa Mugabe a jaka yana gyangyadi bayan ya bar mulki

Ashe $1m aka sacewa Mugabe a jaka yana gyangyadi bayan ya bar mulki

- Kusan dala miliyan daya aka sace wa tsohon shugaban kasar Zimbabwe

- Kamar Yanda jaridar kasar ta ruwaito, tsohon shugaban kasar yace yayi babban rashi

- Ana zargin hadiman shi uku da laifin satar

Ashe $1m aka sacewa Mugabe a jaka yana gyangyadi bayan ya bar mulki

Ashe $1m aka sacewa Mugabe a jaka yana gyangyadi bayan ya bar mulki
Source: UGC

Kusan dala miliyan daya aka sace daga jakar hannun tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe inji jaridar kasar.

Mutane uku suka bayyana da safiyar yau akan zargin da ake musu na sace jakar hannu mai dauke da dala 150,000.

Kamar yanda takardun kotu da jaridar ta gani, tace Mr Mugabe yace yayi rashi mai yawa.

Mr Mugabe, mai shekaru 94, wanda sojojin kasar suka tirsasa shi don sauka kujerar shi a 2017.

Har a wannan lokacin, yayi mulkin kasar na shekaru 37, a matsayin firayem ministan kasar daga baya kuma shugaban kasar.

Ya taba cewa kasar bazata taba durkushewa ba, sun zarge shi rayuwar almubazzaranci yayin shugabantar kasar wanda hakan ya kawo durkushewar tattalin arzikin kasar.

Dalla dallar abinda ya faru yana fitowa ne bayan da kasar ta Zimbabwe take fuskantar tashin gwauran zabi na kayan abinci a satin da ya gabata.

Zanga zangar da mafusatan yan kasar keyi akan tashin kayan abincin ya tirsasa shugaban kasa Emmerson Mnangagway ya fasa tafiyar shi zuwa turai.

Amma Ina kudin ya dosa?

Kamar yanda jaridar ta wallafa kotun ta gano cewa Mr Mugabe ya dau kudin ne don kaiwa kauyan shi a Zvimba a bakar jakar hannu yayin da yake shugaban kasa a 2016.

Anyi zargin ya bawa Constance Mugabe wata yar uwarshi dake aiki agidanshi ajiyar jakar.

GA WANNAN: Wasikar PDP ga duniya: Shugaba Buhari na shirin juyin mulki ta hanyar Kotun Qoli

Sauran wadanda ake zargin ya dauke su ne a matsayin masu gorge gorge a lokacin da akayi satar, wanda ake musu zargin ya faru tsakanin 1 ga watan disamba zuwa farkon watan Janairu 2019.

A watan Maris na shekarar da ta gabata, watanni hudu bayan tsige shi daga kujerar shi, ya tambayi Constance Mugabe ajiyar da ya bada amma tace bata san inda suke ba.

An zargi cewa Mr Mugabe ya umarci sauran ma'aikatan da su dubo jakar. Daga baya anga jakar amma da dala 78,000 a ciki.

Wadanda ake zargi da satar an zarge su da kashe kudaden akan motoci, gidaje da dabbobi.

Tun daga saukar Mugabe kujerar shi yake da matsalar kafa kuma ya dau watanni a Singapore yana ganin likita.

Abinda ba a sani ba shine, yana nan akayi satar ko bayan tafiyar shi?

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel