Marafa ya mika godiyarsa ga Zamfarawa bayan da kotu ya bashi tuta

Marafa ya mika godiyarsa ga Zamfarawa bayan da kotu ya bashi tuta

- Sanata Kabiru Marafa ya jinjinawa babban kotun tarayya akan hukuncin ta

- INEC taki amincewa da jerin yan takarar da wani bangare na jam'iyyar APC ta kai

- Hakan zai kawo karshen tserewa hukunci da jam'iyyun da yan siyasa ke yi

Sanata Kabiru Marafa ya jinjinawa babban kotun tarayya akan yanke hukuncin kin amincewa da dan takarar gwamna a karskashin Jam'iyyar APC da hukumar zabe mai zaman kanta ta.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ki amincewa da jerin yan takarar da wani bangare na jam'iyyar APC a ta jihar Zamfara ta mika sakamakon kin yin zaben fidda gwani da Jam'iyyar tayi.

A maida martanin gaggawa da Sanatan yayi akan hukuncin da Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta yanke, yace hakan ya kawo karshen siyasar da ta kai Gwamna Abdul'aziz Yari kujerar gwamnan jihar ta Zamfara.

Marafa ya mika godiyarsa ga Zamfarawa bayan da kotu ya bashi tuta

Marafa ya mika godiyarsa ga Zamfarawa bayan da kotu ya bashi tuta
Source: Depositphotos

Kotun tace hukumar zabe mai zaman kanta tayi abinda ya dace nakin karbar jerin sunayen yan takarar zabe mai zuwan da wani bangare na APC na jihar Zamfara ta mika.

Mai shari'a Ojukwu, a hukuncin ta na ranar juma'a, tace ba laifin hukumar zaben bane da APC ta kasa yin zaben fitar da gwani a lokacin da aka kayyade musu.

Ojukwu tace abinda INEC tayi zai kawo karshen tsallake hukunci da jam'iyyun siyasa da yan siyasa sukeyi; don tabbatar da bin doka.

KU KRANTA KUMA: 2019: Jirgin Buhari ya isa kudu maso yamma don isar da sakon ‘Next Level’ na APC

An yanke hukuncin ne sakamakon karar da wasu yan jam'iyyar APC wadanda suka ce sun shiga cikin wadanda jam'iyyar ta amince da takarar su a jihar Zamfara.

Marafa yace zai kalubalanci hukuncin babban kotun jihar Zamfara, da ta tabbatar da wani bangaren jam'iyyar karkashin jagorancin Yari sunyi zaben fidda gwanin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel