Bayan janyewar Oby Ezekwesile, sauran kananun ‘yan takara da suka karaya sun Kanye zasu mara wa daya baya

Bayan janyewar Oby Ezekwesile, sauran kananun ‘yan takara da suka karaya sun Kanye zasu mara wa daya baya

- Shugabancin jam'iyun ANN Fema Durotoye da YPP ta Kingsley Moghalu sunyi hadaka

- Sunyi hadakar ne domin ceto Nigeria

- Sunce Nigeria tana bukatar canji wanda ba na fatar baki kadai baShugabancin jamiyun ANN da YPP dai sun kafa jam'iyar hadaka mai suna "the force"

Jamiyun biyu sun ce sun hada kai ne domin kwato kasa Nigeria daga hannun shugabannin da basu cancanta ba kuma suka dakile ta na tsawon lokaci.

Shugaban jamiyar ANN Emmanuel Dania da takwaransa na jam'iyar YPP comrade Bishop Amakiri su suka bayyana haka ga manema labarai a ranar juma'ar da ta gabata.

Bayanin me dauke da sa hannun shugabannin jam'iyun biyu ya kunshi bayanai na yunkurin su kawo cigaba ga kasa.

Bayan janyewar Oby Ezekwesile, sauran kananun ‘yan takara da suka karaya sun Kanye zasu mara wa daya baya

Bayan janyewar Oby Ezekwesile, sauran kananun ‘yan takara da suka karaya sun Kanye zasu mara wa daya baya
Source: UGC

Sukace Nigeria tana cikin wani yanayi na bukatar canji Wanda ba na fatar baki ba sai dai na aiwatar wa daga mutane masu kishin kasa wadanda zasu kwace mulki daga hannun jam'iyar PDP da APC masu rike da kasar na tsawon shekaru tun 1999.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa Buhari yayi gaggawan sallamar shugaban Alkalin Najeriya - Sabon bincike

Sun kara da cewa duk da sun san kwace mulkin ba abu ne me sauki ba amma suna da yakinin samun goyon baya daga daukacin al'ummar Nigeria sama da miliyan 88 masu rayuwa a kasa da dala 1 a rana domin kuwa da hadin kansu ne za a iya fafutukar kwato ta daga hannun bata garin shugabannin.

Sun kara da cewa nan gaba kadan zasu fitar da dan takarar da zai wakilce su a babban zaben shugaban kasa me zuwa. Duk da za a ga cewa sunyi wannan hadakar da wuri amma ba a makara da ceto kasa ba kuma yanzu ne lokacin da ya dace a ceto ta fiye da kowane lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel