Harin Offa: Bindigogi 21 yan fashin suka sace daga caji-ofis kafin harin, shaida ya fadi wa kotu

Harin Offa: Bindigogi 21 yan fashin suka sace daga caji-ofis kafin harin, shaida ya fadi wa kotu

- Sama da bindigogi 21 kirar AK 47 ne sukayi layar zana a ma'ajiyar su a ofishin yan sandan Offa

- Ana zargin dasu akayi amfani wajen fashin da yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 33

- Na'urar daukar hotuna ta sirri ce tasa aka bankado wadanda ake zargin

Harin Offa: Bindigogi 21 yan fashin suka sace daga caji-ofis kafin harin, shaida ya fadi wa kotu

Harin Offa: Bindigogi 21 yan fashin suka sace daga caji-ofis kafin harin, shaida ya fadi wa kotu
Source: Depositphotos

A ranar juma'a ne daya daga cikin shaidun masu kara a shari'ar fashin Offa, sifeta Hitila Hassan, yace an sace sama da bindigogi masu kirar AK 47 ne aka sace a ma'ajiyar bindigogi ta ofishin yan sandan yankin.

Shaidar, wanda mai kara farfesa Wahab Egbewole ya jagoranta yayi maganar ne a komawar da babbar kotun Ilorin tayi don cigaba da sauraron karar.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa sama da mutane 33 wanda ya hada da yan sanda tara, sun rasa rayukan su a mummunan fashi da makamin da akayi a 5 ga watan Afirilu 2018.

Mai shaidar ya nuna mutane biyar dake gurfane a gaban kuliya a matsayin wadanda suka hada kai da babban wanda ake zai, Marigayi Michael Adikwu.

Sune Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez da Niyi Ogundiran.

Ya kuma sanar da kotun cewa na'urar daukar hoto ta sirri dake a bankin ta nuna wadanda ake zargin wanda hakan ne yasa aka damko su.

Hassan, wani jami'i dake tare da kungiyar leken asiri ta sifeta Janar din yan sanda, yace akwai sauran wadanda sukayi fashin da yawa.

Tsohon sifeta Janar ne ya kirkiro kungiyar leken asirin kuma mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari ke shugabantar ta.

Yace kungiyar shi sun je Ilorin ne a karkashin umarnin sifeta janar din yan sanda don su zakulo wadanda sukayi mummunan aikin.

Hassan yace kungiyar shi sunyi aiki ne da ofishin binciken laifuka.

"Mun ziyarci gurin ajiye bindigogi na ofishin yan sandan Offa in da muka gano an dau sama da bindigogi masu kirar AK 47 21. Wadanda ake zargin sunce bayan da marigayi Michael Adikwu ya kammala fashin daga bankin sai ya tunkari ofishin yan sandan in da ya fara ihun cewa yazo daukar fansar korar shi daga aiki da akayi. Daga nan sai ya fara harbi ta ko'ina."

"Bayan mun natsu mun kalla na'urar daukan hotunan sirrin ne muka gano fuskokin su kuma muka yada a kafafen yada labarai don yan Najeriya su taimaka mana don damke su.

Ta haka ne muka samu damke Ibikunle Ogunleye a Oro, karamar hukumar Irepodun ta jihar. Da farko ya musa amma muna nuna mishi shaidar mu, sai ya amsa laifin shi. Kama shi ne yasa muka samu damar kama karin mutane hudu dake gurfane yanzu," in shi.

Da farko, sifeta Yusuf Dauda, mai tsaron kayayyakin shaida na hedkwatar yan sanda a Ilorin ya shaida hakan.

GA WANNAN: Matsalar Tsaro: 'Yan Kamaru 32,000 sun fado Najeriya gudun hijira

Yace a ranar 10 ga watan Afirilu 2018 ne wani tsohon jami'in yan sanda a karamar hukumar Offa, CSP Danjuma Adamu, ya bashi wasu makamai ajiya wadanda ake zargin dasu akayi fashin.

Yace a ranar 15 ga watan Afirilu ne Hassan ya kawo wata Lexus Jeep mai dauke da sunan "Saraki" da makullin ta, wata motar kirar Mercedes Benz mai dauke da sunan "Saraki"

Masu kara sun bayyana duk kayan nan don ganin kotun.

Mai shari'a Halimat Salmat ta daga cigars cigaba da sauraron karar zuwa 19 da 20 ga watan Fabrairu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel