Da dumin sa: Shugaba Buhari ya sake yin wani sabon nadi mai muhimmaci

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya sake yin wani sabon nadi mai muhimmaci

Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da sabon nadin shugaba na rikon kwarya a ma'aikatar dake kula da cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission (NDDC).

Wanda aka ba mukamin dai kamar yadda muka samu shine Farfesa Nelson Braimbraifa.

Nadin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai baiwa shugaban kasa na musamman a fannin yada labarai inda yace nadin ya biyo bayan tattauna maganar a zaman majalisar zartarwar tarayyar.

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya sake yin wani sabon nadi mai muhimmaci

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya sake yin wani sabon nadi mai muhimmaci
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Mafusatan matasa sun farwa jami'an gwamnati a Sokoto

Sauran wadanda sanarwar ta tabbatar da nadin su na rikon kwarya sun hada da Sabon Darektan kudi, Mista Chris Amadi da kuma babban injiniyan hukumar Samuel Adjogbe a matsayin Daraktan ayyuka.

A wani labarin kuma, Amurka da Birtaniya sun ce ba sa goyon bayan kowane dan takara daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaben da za a yi a watan Fabrairun bana.

Amurka ta ce tana sanya ido tare da sauran kasashe kan mutanen da ke katsalandan a harkokin siyasa, ko kuma suke rura wutar muzgunawa 'yan kasa gabanin zaben, ko da lokacin da ake yinsa ko bayan sa.

Burtaniya kuwa ta ce 'yan Najeriya ne kawai za su iya zabar wanda zai shugabance su, ta hanyar lumana da zabe na gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel