Abubuwa 8 da Buhari ya fadi kan Jastis Walter Onnoghen yayinda ya sallameshi

Abubuwa 8 da Buhari ya fadi kan Jastis Walter Onnoghen yayinda ya sallameshi

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen

- Shugaban kasan ya saki jawabi inda yayi bayanin abinda ya wajabta masa sallamarsa

Ga abubuwa 8 da shugaba Buhari ya fada a jawabinsa:

1. Zargin boye wasu dukiyoyin da ya mallaka

Shugaba Buhari yace: "Kasar nan ta shiga cikin rudani kan zargin babban alkalin Najeriya da rashawa tun lokacin da wata kungiyar fafutuka ta fallasa shi."

2. An gano wasu kudade daban da ya boye

Shugaba Buhari ya ce bayan zargin rashin bayyana wasu asusun bankinsa, an gano wasu cinikayya da yayi na miliyoyin dala wanda bai bayyana ba bisa doka.

3. Onnoghen ya gaskata zargin da ake masa

Shugaba Buhari ya ce gaskata zargin da akayi masa na daya daga cikin manyan dalilan da yasa aka sallamesa.

4. Kin murabus bayan tabbatar da zargin da ake masa

Shugaban Buhari yace: "Abinda mukayi tunani shine bayan hannunsa yayi dumu-dumu cikin rashin gaskiya da kuma gaskatawan da yayi, Jastis Walter Onnoghen zai kare mutuncin bangaren shari'a ta hanyar sauka daga kujerarsa."

5. Kokarin kotuna daban-daban na kare Walter Onnoghen

Shugaba Buhari ya zargi Walter Onnoghen da yin amfani da kotuna daban-daban domin kare kansa da kokari hana kotun CCT gurfanar da shi

6. Walter Onnoghen bai fi karfin doka ba

Shugaba Buhari yace: "Najeriya kasar demokradiyya ce kuma babu wanda yafi karfin doka.

7. Ya kasance yana wanke wadanda aka kamasu dumu-dumu cikin laifuka

Shugaba Buhari ya zargi Jastis Walter Onnoghen da laifin amfani da karfinsa wajen wanke wasu mutane da aka kama da kashi a gindi cikin rashawa.

8. Umurnin kotun CCT

Shugaba Buhari yace: "An nada sabon shugaba Alkalan ne bisa ga umurnin da kotun hukunta ma'aikatan Najeriya wato CCT tayi inda ta umurci shugaban kasa ya nada babban Alkali a kotu koli a matsayin shugaban Alkalai kuma shugaban majalisan shari'a."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel