Musulmai sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya shafa a Amurka

Musulmai sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya shafa a Amurka

Yayin da Ma’aikatan kasar Amurka ke cigaba da fuskantar barazana daga gwamnati, mun ji labarin yadda Musulman kasar su kayi namijin kokari wajen rabawa jama’a abinci kyauta domin su samu sauki.

Musulmai sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya shafa a Amurka

Musulma Amurka sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya taba
Source: Facebook

Kungiyar ma’aikatan sufurin yankin Boston da sauran ma’aikatan da su ke fama da matsalar rashin albashi a dalilin rufe ayyukan gwamnati da aka yi sun samu agaji daga wasu Bayin Allah Musulmai da ke kasar Amurka a yanzu.

Wata kungiya ta musulman da ke zama a Nahiyar Amurka ce ta kawowa jama’a dauki na kayan abinci da nama na akalla Dala 20. An raba abincin ne daga wani kamfanin abinci mai suna Quincy International Foods da ke US.

Akalla ma’aikata 1000 da ke aiki a filin jirgin sama na Jihar Boston wanda yanzu albashin su ya makale ne su ka amfana daga wannan sadaka da Musulmai su ka rika rabawa na kayan abinci da nama da dai sauran kayan tabawa a lashe.

KU KARANTA: Buhari na shirin yin juyin mulki da tsige CJN Onnoghen - PDP

Musulman sun yi alkawari cewa nan gaba za a rika raba kati da sauran abubuwan da za su ragewa jama’a radadi a daidai wannan lokaci da albashin su ya makale inji Darektan wannan kungiya ta Musulmai, Malaika McDonald.

Sama da ma’aikata 8000 da ke aiki da gwamnatin tarayya a garin Massachusetts ba su samu albashin su ba. Dole ta sa musulmai da sauran kungiyoyi su ka kawo masu agaji ganin cewa wannan abu ya shafi na kusa da su da Abokan arziki.

Yanzu dai ana ta faman rikici da shugaban kasar Amurka Donald Trump da mutane inda har ta kai ma’aikata sun yi makonni kusan 5 babu labarin albashi. Yunkurin gina Katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico ne ya jawo sabanin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel