Babban basarake a Adamawa ya koma fadarsa da 'yan Boko Haram suka lalata

Babban basarake a Adamawa ya koma fadarsa da 'yan Boko Haram suka lalata

Daga karshe hakimin Michika, Ngida Zakawa Kwache ya koma fadarsa bayan shekaru biyar da nadinsa.

An zabi Ngida Kwache a matsayin hakimin Michika ne a ranar 31 ga watan Disambar 2013 amma kungiyar Boko Haram ta kwace Michika a Satumban 2014.

Garin ya kasance karkashin ikon kungiyar Boko Haram kafin dakarun sojojin Najeriya su kwace garin a ranar 29 ga watan Janairun 2015.

Sai dai fargaban Boko Haram ya saka an rufe ofishin hakimin amma an bude a ranar Alhamis da ta gabata.

Babban basarake a Borno ya koma fadarsa da 'yan Boko Haram su ka lalata

Babban basarake a Borno ya koma fadarsa da 'yan Boko Haram su ka lalata
Source: UGC

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Ngida Kwache, jika ne ga wanda ya kafa garin Michika, Kwada Kwakaa kuma shine dan asalin garin na farko da ya fara mulki tun bayan samun 'yancin Najeriya daga turawan mulkin mallaka.

Hakimin da ya gabace shi, Mohammed Maude ya rike mukammin hakimin garin na rikon kwarya har na tsawon shekaru 53 kafin rasuwarsa.

"A lokacin da turawan mulkin mallaka za su koma kasarsu, suna bukaci nada hakimi da zai mulki garin.

"An gudanar da zabe kuma kawu na (Stephen Konkikwara) ne ya lashe zaben amma suka ce ya yi yaranta kuma ba shi da aure.

"Sai nada wani a matsayin shugaban rikon kwarya. Ya yi mulki na tsawon shekaru 53 har zuwa lokacin da ya rasu a 2013."

A wurin taron bude fadar, Shugaban karamar hukumar MIchika, Mathew Vendi Favandzaer ya ce an umurce shi ya mika fadar ga Ngida Kwache saboda ya cika ka'idojin zama hakimin garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel