Dakatar da Onnoghen wuce gona da iri ne a salon mulkin kama-karya - Atiku

Dakatar da Onnoghen wuce gona da iri ne a salon mulkin kama-karya - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dakatar da Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen Walter Nkanu Samuel Onnoghen a matsayin aikin kama-karya mai muni.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a 25 ga watan Janairu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da Justice Onnoghen ne a dakin taron Majalisa da ke Fadar Aso Rock a ranar Juma'a.

Shugaban kasar ya nada Justice Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukadashin Alkalin Alkalan na kasa.

Dakatar da Onnoghen wuce gona da iri ne a salon mulkin kama-karya - Atiku

Dakatar da Onnoghen wuce gona da iri ne a salon mulkin kama-karya - Atiku
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa sunayen gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Ga wani bangare cikin sanarwar na Atiku:

"Dakatar da CJN da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ya sabawa tsarin demokradiyya wadda ban amince da shi ba kuma ina kira da Justice Onnoghen da fannin shari'a na kasa suyi amfani da duk abinda za su iya yi na doka domin ganin dakatarwar ba ta dore ba.

"Wannan yana daya daga cikin ayyukan da gwamnati mai ci yanzu da wasu mikya demokradiyya ke aikatawa domin ruguza demokradiyyar da muka sha wahala wurin samarwa tare da yunkurin Shugaba Buhari na murde zabe musamman yanzu da ranar 16 ga watan Fabrairu da ke matsowa.

"Maganar tuhumar da ake yiwa Cif Justice Walter Onnoghen tana gaban kotu kuma kawo yanzu, kotun ta bawa Justice Onnoghen gaskiya. Saboda haka, me yasa ba za a bari kotu da kammala shari'ar a kan batun ba? Gaggawar mene ake yi?

"Ina son yin amfani da wannan damar inyi kira ga lauyoyi su hada kansu. Kada ku bari Shugaba Buhari ya raba kawunnan ku. Fannin shari'a ita ce mataki na karshe da talaka ke dogora ta ita kuma ita ce za ta kare mana demokradiyyar mu.

"Sako na ga 'yan Najeriya shine su mike tsaye suyi tawaye ga wannan matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na yaki da fannin shari'ar mu. Kasar mu tana ta lalacewa a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, lokaci ya yi da zamu ceto demokradiyyar mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel