Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Jim kadan bayan sallaman Shugaban Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon Alkalin alkalai mai suna Jastis Ibrahim Tanko Mohammed.

Legit.ng Hausa ta samu wannan rahoto ne daga fadar shugaban kasa ta Aso Villa inda tace: " Da ranan nan, shugaba Buhari ya nada Jastis Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashin shugaba Alkalan Najeriya."

"An nada sabon shugaba Alkalan ne bisa ga umurnin da kotun hukunta ma'aikatan Najeriya wato CCT tayi inda ta umurci shugaban kasa ya nada babban Alkali a kotu koli a matsayin shugaban Alkalai kuma shugaban majalisan shari'a."

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

KU KARANTA: Gwamnati tarayya ta bukaci shugaban Alkalai, Walter Onnoghen, yayi murabus

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya gaisa da Jastis Muhammadu Tanko
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari yayina yake rattaba hannun kan takardan nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Jastis Muhammadu Tanko yayinda aka nada shi matsayin Shugaban Alkalan Najeriya
Source: UGC

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Jastis Muhammadu Tanko matsayin Shugaban Alkalan Najeriya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel