Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya nada Ibrahim Tanko Muhammed mukaddashi

Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya nada Ibrahim Tanko Muhammed mukaddashi

Labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Legit.ng ta samu wannan rahoto ne daga bakin hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafofin sada zumunta. Bashir Ahmad inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da shugaban alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, kuma ya nada Mr Ibrahi Tanko Muhammed matsayin mukaddashin Alkalin alkalai."

"Shugaba Buhari ya sallameshi ne bisa ga umurnin kotun hukunta ma'aikatan gwamnati CCT"

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kuma dai, shugaban Alkalan Najeriya ya ki bayyana a kotu

Mun kawo muku rahoton cewa Lauyan gwamnatin a shari'ar Jastis Walter Onnogehn, Aliyu Umar, ya bayyana a ranan Talata cewa gwamnati ta bukaci Alkalin ya sauka daga kujeransa kawai.

Barista Umar yayinda yake jawabi da safen nan a gaban kotun CCT ya ce an aikawa Alkali Walter Onnoghen takardan gayyata amma basu san ko ya karba ko kuma bai samu ba.

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

KU KARANTA: Kuma dai, shugaban Alkalan Najeriya ya ki bayyana a kotu

Wadannan asusu sune:

a. Account No. 5001062686 (Euro) Standard Chartered Bank (SCB)

b. Account No 5001062679 (Pound Sterling) SCB

c. Account No 0001062650 (Dollar) SCB

d. Account No 0001062667 (Naira) SCB, and

e Account No 5000162693 (Naira)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel