2019: Atiku ya ci zabe ya gama domin mutanensa sun fi na Buhari yawa – Buba Galadima

2019: Atiku ya ci zabe ya gama domin mutanensa sun fi na Buhari yawa – Buba Galadima

- Alhaji Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa Atiku ya gama lashe zaben da za a a watan gobe saboda yadda ya samu karbuwa a wajen al'ummar Najeriya

- Galadima yayi hasashen cewa dan takarar na PDP ya fi Buhari yawan jama'a a wajen kamfen dinsu

- Ya kuma zargi shugaba Buhari da amfani da kudi wajen tara jama'a a lokacin kamfen dinsa

Tsohon jigon jam’iyyar All Progressives Congress kuma daya daga cikin manyan masu goyon bayan takarar Atiku Abubakar a yanzu, Alhaji Buba Galadima, ya ce dan takararsu ya gama lashe zaben da za a a watan gobe saboda yadda ya samu karbuwa a wajen al'ummar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu a birnin Landan, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

2019: Atiku ya ci zabe ya gama domin mutanensa sun fi na Buhari yawa – Buba Galadima

2019: Atiku ya ci zabe ya gama domin mutanensa sun fi na Buhari yawa – Buba Galadima
Source: Depositphotos

Buba Galadima ya ce suna godiya ga 'yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu a tarukan yakin neman zabe da ke gudana a fadin kasar.

"Kuma idan dai kuri'ar dan Najeriya ita za ta tabbatar da cin zabe, to mun gama cin zabe," in ji shi.

Har ila yau, ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya fi Shugaba Buhari tara jama'a a lokutan yakin neman zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa jami'an INEC 2 shekaru 7 a gidan yari kan karban cin hanci daga Diezani

Galadima ya kuma zargi shugaba Buhari da amfani da kudi wajen tara jama'a a lokacin kamfen dinsa.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa cewa kudi ne suka sa shi komawa wurin Atiku Abubakar, inda ya ce: "Buhari bai taba ba ni koda sisin kwabo ba, to idan shi a lokacin bai ba ni ba, to ya za a ce a yanzu wani zai saye ni."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel