Badakalar N5bn: Tsohon gwamnan Gombe zai san makomarsa ranar 22 ga watan Maris

Badakalar N5bn: Tsohon gwamnan Gombe zai san makomarsa ranar 22 ga watan Maris

- Mai shari'a Babatunde Quadri na babbar kotun tarayya ya sanya ranar 22 ga watan Maris, 2019, a matsayin ranar yanke hukunci ga tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje

- Goje na fuskantar shari'a ne tare da tsohon shugaban hukumar ilimi bai daya ta jihar, Aliyu El-Nafaty; S.M. Dokoro, bisa zarginsu da sama da fadi da N5bn

- Haka zalika an yi zargin cewa suna da hannu dumu dumu a bayar da kwangilar samar da abinci a gidan gwamnatin jihar Gombe a lokacin da Goje yake gwamnan jihar

Mai shari'a Babatunde Quadri na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Jos, jihar Filato, ya sanya ranar 22 ga watan Maris, 2019, a matsayin ranar yanke hukunci ga tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje, kan zargin da ake masa na sama da fadi da wasu makudan kudade.

Goje, wanda a yanzu dan majalisar dattijai ne, yana fuskantar shari'a ne tare da tsohon shugaban hukumar ilimi bai daya ta jihar, Aliyu El-Nafaty; S.M. Dokoro, da kuma dan uwan tsohon gwamnan, Sabo Tumu, bisa zarginsu da sama da fadi da N5bn.

An yi zargin cewa suna da hannu dumu dumu a cikin wawushe kudaden, da kuma bayar da kwangilar samar da abinci a gidan gwamnatin jihar Gombe a lokacin da Goje yake gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Sabon rikici: Kotun tarayya da babbar kotun Gusau sunyi sabani a shari'ar APC da INEC a Zamfara

Badakalar N5bn: Tsohon gwamnan Gombe zai san makomarsa ranar 22 ga watan Maris

Badakalar N5bn: Tsohon gwamnan Gombe zai san makomarsa ranar 22 ga watan Maris
Source: Depositphotos

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta hannun lauyanta, Wahab Shittu, ya rufe shari'arsu da wadanda ake zargin a ranar 31 ga watan Mayun 2018, bayan kiran shaidu 25 tare da kuma gabatar da takardu a matsayin hujjar shari'ar.

Shi kuwa da ya bude shari'ar, lauyan Goje, Chris Uche, SAN, a ranar 14 ga watan Satumba, ya shigar da kara maras bukatar doguwar shari'a.

A zaman da kotun ta yi ranar Juma'a, Uche ya bayyanawa kotun cewa mutuwar Tumu ta lalata takardun hujjar da aka gabatar la'akari da rahotan rundunar 'yan sanda na cewar ya mutune sakamakon hatsari da ya rutsa da shi.

Mai shari'a Quadri, domin hakan, ya dage sauraron karar har sai ranar 22 ga watan Maris, 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel