Da yiwuwan a saki Dasuki, kotu ta nada kwamiti na musamman kan duba al'amarinsa

Da yiwuwan a saki Dasuki, kotu ta nada kwamiti na musamman kan duba al'amarinsa

Wata babban kotun birnin tarayya Abuja ta nada kwamiti mutane uku domin shawo kan rashin jituwan da aka samu kan shari'ar Sambo Dasuki na zargin almundahana da babakeren biliyoyin kudin makamai.

An nada sabuwar kwamiti karkashin jagorancin jastis Hussein Baba-Yusuf domin shawo kan al'amarin da kuma yadda za'a iya cigaba da shari'ar.

Kanal Sambo Dasuki (Mai ritaya) ya kasance a tsare hannun hukumar tsaron SSS tun watan Disamban 2015 duk da cewa kotuna daban-daban guda shida sun bayar da belinsa.

A wata wasika da ya aikawa kotun, ya bayyana cewa ba zai sake bayyana a kotu ba domin nuna rashin yardarsa da yadda gwamnatin tarayya ke sabawa umurnin kotu na sakesa. Ya ce gwamnatin tarayya ba ta hakkin cigaba da tsareshi bayan kotu ta ce a sake shi.

KU KARANTA: Mutane a Yobe sun shiga rudanni bayan sojoji sun tsere

Shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai saki Kanal Sambo Dasuki ba muddin mutane na mutuwa kulli yaumin a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Sambo Dasuki, wanda ya kasance tsohon mai bada shawara kan tsaron kasa yana gurfana a kotu ne bisa ga zargin karkatar da kudaden da aka bashi domin sayawa sojoji msu yakan Boko Haram makamai.

Dasuki ya rabawa abokan siyasa wadannan kudi domin yakin neman zaben tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel