Sabon rikici: Kotun tarayya da babbar kotun Gusau sunyi sabani a shari'ar APC da INEC a Zamfara

Sabon rikici: Kotun tarayya da babbar kotun Gusau sunyi sabani a shari'ar APC da INEC a Zamfara

- Babbar gwamnatin tarayya da ke Abuja, a ranar Juma'a ta haramtawa jam'iyyar APC gabatar da 'yan takararta a Zamfara a zaben 2019 da ke gabatowa

- Wannan hukuncin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu da ke Gusau ta yanke a yau na cewa jam'iyyar APC na da 'yan takara a Zamfara

- Idan za a iya tunawa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta haramtawa APC daga gabatar da 'yan takara a kujeru daban daban a jihar Zamfara

Rahotannin da Legit.ng ta samu yanzu na nuni da cewa babbar gwamnatin tarayya da ke Abuja, a ranar Juma'a ta haramtawa jam'iyyar APC gabatar da 'yan takararta a Zamfara a zaben 2019 da ke gabatowa.

Wannan hukuncin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu da ke Gusau ta yanke a yau, bisa jagorancin mai shari'a Muhammad Bello Shinkafi, inda ta tabbatar da cewa jam'iyyar APC na da 'yan takara a Zamfara kasancewar ta gudanar da zaben fitar da gwani a ranar 3 zuwa 7 ga watan Oktoba, 2018.

KARANTA WANNAN: Kasa da kwanaki 25 ga zaben 2019: Yan takara sun maka INEC kotu kan dokokin zabe

Sabon rikici: Kotun tarayya da babbar kotun Gusau sunyi sabani a shari'ar APC da INEC a Zamfara

Sabon rikici: Kotun tarayya da babbar kotun Gusau sunyi sabani a shari'ar APC da INEC a Zamfara
Source: Twitter

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu na babbar kotun gwmanatin tarayya, Abuja, ya tabbatar da cewa hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yanke yayi dai dai na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a Zamfara da za su shiga zaben 2019.

Mai shari'a Ojukwu ya bayyana cewa matakin da INEC ta dauka kan batun zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC ta gudanar a Zamfara ya yi dai dai ko da kuwa an jingina shi da shari'a, kuma zai taimaka wajen isar da sakon gargadi da darasi ga sauran jam'iyyu a nan gaba.

Idan za a iya tunawa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta haramtawa APC daga gabatar da 'yan takara a kujeru daban daban a jihar Zamfara, akan abunda hukumar ta kira gazawar jam'iyyar na gudanar da zaben fitar da gwani a cikin wa'adin da hukumar ta kayyadewa jam'iyyu.

Sai dai tun a lokacin, APC bata gamsu da wannan mataki na hukumar zaben ba, inda ta shigar da kara kotu domin neman 'yancinta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel