Gwamnatin jihar Kogi ta rufe dukkan kafofin sadarwar MTN, ta bayar da dalili

Gwamnatin jihar Kogi ta rufe dukkan kafofin sadarwar MTN, ta bayar da dalili

Hukumar dake tattara haraji na jihar Kogi dake a shiyyar Arewa ta tsakiya watau Kogi State Internal Revenue Service (KGIRS) ta ruffe dukkan kafofin sadarwar kamfanin MTN a jihar saboda rashin biyan harajin da ya kai Naira miliyan 120.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da gwamnatin jihar ta fitar tana bai bayyana dalilin rufe kamfanin na MTN dauke da sa hannun babban Daraktan shari'a na hukumar tattara haraji na jihar Barista Jamil Isah.

Gwamnatin jihar Kogi ta rufe dukkan kafofin sadarwar MTN, ta bayar da dalili

Gwamnatin jihar Kogi ta rufe dukkan kafofin sadarwar MTN, ta bayar da dalili
Source: UGC

KU KARANTA: An zargi Lai Muhammad da badakalar Naira biliyan 2.5

Legit.ng Hausa ta samu cewa hukumar ta KGIRS bayyana cewa sun dade suna takun saka da kamfanin na MTN don kuwa ko a watan Oktoban da ya shude kotu ta tilastawa kamfanin ya biya harajin sa ga gwamnatin jihar amma sai kamfanin yayi fatali da umurnin.

Sanarwar ta cigaba da cewa, a lokacin da kotun ta umurci MTN ta biya harajin ta na Naira miliyan 120, sai ta dauki matakin renawa gwamnatin hankali inda ta biya Naira dubu 250 kacal wanda hakan ne ya harzuka gwamnatin ta dauki matakin rufe MTN din.

Kamar dai yadda muka samu, tuni al'ummar jihar suka soma kokawa na rashin kamfanin a jihar inda wasu da dama suka soma sauya layuyyukan su da wasu kamfanonin sadarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel