Mafusatan matasa sun afkawa tawagar jami'an gwamnati a jihar Sokoto

Mafusatan matasa sun afkawa tawagar jami'an gwamnati a jihar Sokoto

Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan jam'iyya mai mulki ne ta Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto dake a Arewa maso yammacin Najeriya sun farwa tawagar babbar Kwamishiniyar dake kula da hukumar 'yan gudun hijira ta gwamnatin tarayya da tawagar ta.

Lamarin dai ya auku ne sadda kwamishiniyar hukumar ta National Commission for Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons (NCRMIDP), Hajiya Sadiya Umar Farouk ta ziyarci garin karamar hukumar Gandi domin kaddamar da bayar da wasu kaya ga 'yan gudun hijira.

Mafusatan matasa sun afkawa tawagar jami'an gwamnati a jihar Sokoto

Mafusatan matasa sun afkawa tawagar jami'an gwamnati a jihar Sokoto
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An ce EFCC ta binciki Lai Muhammad

Legit.ng Hausa ta samu cewa jim kadan bayan an soma bikin rarraba kayayyakin sai kawai matasan dauke da makamai da sanduna da duwatsu suka zo wurin suka watsa taron, jami'an gwamnatin kuma suka ranta a na kare.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa mafusatan matasan da suka zo wajen taron sun yi ta rera wakokin yabo ga 'yan takarar shugabancin kasa da kuma na gwamnan jihar ta Sokoto, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Aminu Tambuwal.

Ganau ya shaidawa majiyar mu cewa matasan sun farfasa motoci da dama a wurin wanda har sai dai jami'an tsaro suka zo sannan kura ta lafa.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan tireda masu kananan sana'o'i a karkashin inuwar kungiyar 'Nigerian Traders For PMB' sun sha alwashin tarawa shugaba Muhammadu Buhari kuri'u akalla miliyan 10 daga dukkan sassan kasar nan a babban zaben gama-gari da za'a gudanar a watan fabrerun wannan shekarar.

Wannan alkawarin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Mista Yarima Paul Ikonne ta kuma rabawa manema labarai ciki hadda majiyar mu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel