Kasa da kwanaki 25 ga zaben 2019: Yan takara sun maka INEC kotu kan dokokin zabe

Kasa da kwanaki 25 ga zaben 2019: Yan takara sun maka INEC kotu kan dokokin zabe

- A yayin da zaben 2019 ya rage sauran kasan da kwanaki 25 wasu 'yan takara sun maka hukumar INEC a babbar kotun gwamnatin tarayya, Abuja

- Yan takarar sun gabatarwa kotun wannan bukatar ne tare da rokon kotun da ta dakatar da INEC daga amfani da dokokin zaben 2019 da ta tsara yin amfani da su

- Dr Breakforth Onwubuya, wanda ya yi magana a madadin sauran 'yan takarar, ya roki kotu da ta bincika ko INEC tana da ikon gabatar da sabbin dokoki da tsare tsare na gudanar da zabe

A yayin da zaben 2019 ya rage sauran kasan da kwanaki 25, wanda zai gudana a wata mai zuwa, wasu 'yan takara da ke neman kujeru daban daban karkashin inuwar 'Concerned 2019 Elections Candidates (CEC)' sun maka hukumar INEC a babbar kotun gwamnatin tarayya, Abuja, inda suka roki kotun da ta dakatar da INEC daga amfani da dokokin zaben 2019 da ta tsara yin amfani da su.

Kudirin INEC na amfani da dokokin zaben 2019 ya zama abun cece kuce a fadin kasar, inda har kungiyar gamayyar jam'iyyun adawa (CUPP) suka yi ikirarin cewa INECT ta sauka daga turbar da aka santa a baya, tare da jaddada bukatar da ke akwai na INEC ta yi amfani da dokokin zaben 2015 a yayin da zata gudanar da zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon - Nafisa Abdullahi

Kasa da kwanaki 25 ga zaben 2019: Yan takara sun maka INEC kotu kan dokokin zabe

Kasa da kwanaki 25 ga zaben 2019: Yan takara sun maka INEC kotu kan dokokin zabe
Source: Facebook

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma'a a Abuja, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar FJP, Dr Breakforth Onwubuya, wanda ya yi magana a madadin sauran 'yan takarar, ya roki kotu da ta bincika ko INEC tana da ikon gabatar da sabbin dokoki da tsare tsare na gudanar da zabe.

Onwubuya, a cikin wata takarda wacce ya karanta kuma ya rabawa manema labarai a madadin jam'iyyar FJP da sauran 'yan takarar jam'iyyu, Sunday Ezema Esq., ya ce idan har kotu ta tabbatar da cewa INEC na da ikon yin amfani da dokokin zaben, to ya kamata ta kotun ta umurci INEC ta wallafa bayanai na dokoki, tsare tsare da ka'idojin zaben 2019 har sai kowa ya fahimta.

Ya ce: "Wannan matakin da muka dauka ya ta'allaka ne akan sashe na 153 na dokar zabe, wacce ta baiwa INEC umurnin rabawa kowa dokoki da tsare tsare na gudanar da zabe. Abunda muke nufi a nan shine, lallai ya zama wajibi INEC ta cire mutane daga cikin duhun da suke akan dokoki da ka'idojin zaben 2019."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel