Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

Jam’iyyun siyasa guda Talatin da hudu,34, sun yanke shawarar mara ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku, kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar lemar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya a yayin zaben 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jam’iyyun sun yanke wannan shawara ne a karkashin hadaddiyar kungiyarsu ta CUPP, bayan wata doguwar tattaunawa da suka yi shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel a gidansa dake Sagamu.

KU KARANTA: 2019: Yan takaran Jam’iyyar APC sun yi barazanar tayar da hankali a zaben jahar Ribas

Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

Gbenga da Jam'iyyu
Source: UGC

A jawabinsu, shuwagabannin jam’iyyun sun tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta gaza, don haka suke goyon bayan Atiku Abubakar tare da burin zai tsallakar da Najeriya zuwa tudun mun tsira, ta yadda zaman lafiya da sabon arziki zai dawwama a kasar.

Wannan taro na tattaunawa ya samu wakilan kungiyar Yarbawa, Afenifere, kungiyoyin Hausawa, Inyamurai, har ma da na jama’an yankin kudu maso kudancin kasar. Shima a jawabinsa, shugaban jam’iyyar PPN, Cif Razak Eyiowuawi yace manufarsu itace a ceto Najeriya daga matsalar tsaro.

“Ya kamata mu ceto Najeriya daga halin rashin tsaro, tashe tashen hankula da halin matsanancin rayuwa da a yanzu yan Najeriya ke fama dashi a kullu yaumin, hanya daya ta warware matsalolin nan itace kawar da APC daga mulki ta hanyar zama tsintsiya madaurinki daya.” Inji shi.

Samun tagomashi: Jam’iyyu 34 sun yanke hukuncin mara ma Atiku baya a 2019

Gbenga daJam'iyyu
Source: UGC

Ra’ayin sauran shuwagabannin jam’iyyun da suka bayyana a yayin taron bai bambamta dana Cif Razaki ba, inda dukkaninsu sun yi kira dasu hada karfi da karfe wajen taimaka ma Atiku ya kayar da Buhari a zaben 2019.

A jawabinsa, Gbenge Daniel, ya gode ma kungiyoyin da wannan kwarin gwiwa da suka baiwa tafiyar Atiku, inda ya jaddada akwai bukatar hada hannu da duk yan kasa nagari waje kawo sauyi a halin da kasar Najeriya ta tsinci kanta.

A wani labarin kuma, babbar kungiyar inyamurai, Ohanaeze Ndigbo ta yanke shawarar goyon bayan takarar Atiku Abubakar, don haka tayi kira ga Inyamurai dake fadin duniya su zabi Atiku a zaben ranar 16 ga watan Feburairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel