'Yan tireda sun sha alwashin yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri'u miliyan 10

'Yan tireda sun sha alwashin yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri'u miliyan 10

Wasu 'yan tireda masu kananan sana'o'i a karkashin inuwar kungiyar 'Nigerian Traders For PMB' sun sha alwashin tarawa shugaba Muhammadu Buhari kuri'u akalla miliyan 10 daga dukkan sassan kasar nan a babban zaben gama-gari da za'a gudanar a watan fabrerun wannan shekarar.

Wannan alkawarin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Mista Yarima Paul Ikonne ta kuma rabawa manema labarai ciki hadda majiyar mu.

'Yan tireda sun sha alwashin yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri'u miliyan 10

'Yan tireda sun sha alwashin yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri'u miliyan 10
Source: Twitter

KU KARANTA: Kungiyar PDP ta yi hadin gwuiwa da APC don zabar Buhari

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa kungiyar ta kuma mayar wa da tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo martani game da kalaman sa ga shugaba Buhari inda ta shawarci 'yan Najeriya da su yi watsi da 'soki-burutsun-sa'.

Da yake karin haske game da yadda suka shirya samarwa Shugaba Buhari kuri'un miliyan 10, Shugaban kungiyar yace dukkan 'ya'yan kungiyar sun yi alkawarin jawo hankalin 'yan uwan su da abokai da ma makwafta wajen zabar APC a zaben da za'a gudanar.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta tabbatar da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau ndependent National Electoral Commission (INEC) ta dauka kan kin saka jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara zaben 2019.

A yayin da yake yanke hukunci kan karar dake gaban sa, Alkalin kotun Mai shari'a Ijeoma Ojukwu a ranar Juma'a, yace tabbas hukumar zaben ta kasa tayi daidai akan hukuncin da ta dauka na kin karbar sunayen 'yan takara daga APC a jihar ta Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel