Rikicin kabilanci ya janyo salwantar rayuka da asarar dukiya ta miliyoyin naira a Nassarawa

Rikicin kabilanci ya janyo salwantar rayuka da asarar dukiya ta miliyoyin naira a Nassarawa

Wasu gungun yan bindiga sun kai wata mummunar farnaki a unguwar Tudun Uku dake cikin karamar hukumar Toto ta jahar Nassarawa inda suka kashe akalla mutane uku, tare da babbaka gidajen mutane kurmus, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan maharan sun shiga unguwar ne da sanyin safiyar Juma’a, 25 ga watan Janairu, inda shigarsu keda wuya suka kaddamar da hari akan jam’an unguwar tudun uku, inda suka kashe mutane 3, sa’annan suka kona gidaje 7.

KU KARANTA: Kasar Swiss ta maido ma Najeriya $1,000,000,000 daga kudaden da Abacha ya boye a can

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tamkar rikicin kabilanci ne ya sabbaba wannan hari, sakamakon akwai tsohuwar tsatstsamar dangantaka tsakanin yan kabilar Bass da yan kabilar Egbura, kamar yadda shugaban karamar hukumar Toto ya tabbatar.

Shugaban mai suna Nuhu Dauda ya bayyana cewa “Na samu rahoton cewa yan mahara daga kabilar Bassa sun kai farmaki unguwar Tudu Uku dake cikin karamar hukumar Toto, inda suka kashe mutane 3, suka kona gidaje 7, da ababen hawa.

“Haka zalika akwai rahoton dake nuna har yanzu ba’a san inda wani karamin yaro ya shiga ba, tun bayan barkewar rikicin aka nemeshi aka rasa, sa’annan maharan sun fille kan wani mutum guda.” Inji shi.

Dauda ya bayyana bacin ransa sosai game da wannan hari, inda ya kara da cewa abin takaici ne mutane su dinga kare hari akan abokan zamansu, don haka yayi kira da kowa ya mayar da wukarsa, su tuba su zauna lafiya da juna.

Idan za’a tuna, a kwanakin baya babban kwamandan aikin tabbatar da tsaro a jahar Nassarawa, Benuwe da Taraba, Operation Wild stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyana cewa sun kwato manyan bindigu 45 da alburusai 710 daga sansanin yan bindigan kabilar Bassa a kauyen Zwere cikin karamar hukumar Toton jahar Nassarawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel