Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa jami'an INEC 2 shekaru 7 a gidan yari kan karban cin hanci daga Diezani

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa jami'an INEC 2 shekaru 7 a gidan yari kan karban cin hanci daga Diezani

- Wata babbar kotun tarayya da ke Lagas ta yanke wa jami'an INEC biyu shekaru bakwai a gidan yari

- An yanke masu hukuncin ne bayan an kama su da hannu dumu-dumu wajen karban cin hancin daga tsohuwar ministar

- Jami'an da aka yanke wa hukuncin sune Mista Christian Nwosu da Mista Tijani Bashir

Wata babbar kotun tarayya da ke Lagas a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu ta yanke wa wani tsohon sakataren hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Kwara Mista Christian Nwosu da wani tsohon jami’in INEC Mista Tijani Bashir shekaru bakwai a gidan yari.

An tattaro cewa jami’an sun karban cin hanci kudi har naira miliyan 264 daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke, don yin magudin zaben 2015.

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa jami'an INEC 2 shekaru 7 a gidan yari kan karban cin hanci daga Diezani

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa jami'an INEC 2 shekaru 7 a gidan yari kan karban cin hanci daga Diezani
Source: Depositphotos

An yanke masu hukuncin ne bayan an kama su da hannu dumu-dumu wajen karban cin hancin daga tsohuwar ministar.

Justice Mohammed Idris na babbar kotun tarayyah, Lagas, ya tsare Nwosu bayan hukumaryaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta yi zargin cewa ya karbi naira miliyan 30 daga tsohuwar ministar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: APC ta yi babban rashi yayinda tsohon Gwamna Nwobodo ya koma PDP

A baya mun ji cewa Allison Madueke, ministan man fetur na tsohon shugaban Goodluck Jonathan ta alankata tare da wasu ‘yan jami’an INEC da aka zargi da maganan cin hanci a lokacin zaben shekara 2015 wanda jami’yyar PDP suka rasa da mulki ya fado a hannu ‘yan jami’yyar APC.

Christian Nwosu yana daga cikin mutane 3 ‘yan jami’an INEC da Hukumar Laifukan na tattalin arziki EFCC suka gufanar da a ranar Laraba, a gaban alkali MB Idris na babbar kotun tarayya a Ikoyi, Legas, a kan wasu caji 7 na samun tukwici da yake miliyan N265.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel