Ka tsarkake wannan bangare na sharia a gwamnatin - Abubakar Tsav ga sabon Cif Jastis

Ka tsarkake wannan bangare na sharia a gwamnatin - Abubakar Tsav ga sabon Cif Jastis

- Tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Legas ya shawarci mukaddashin alkalin alkalai da ya kawo gyara tare da tsaftace ma'aikatar shari'a

- Ya nuna damuwar shi akan yanda wasu suka maida dakatar da Onnoghen siyasa da kabilanci

- Babu wanda yafi karfin shari'a, ya rage gareshi da yaje ya wanke kanshi gaban kuliya

Ka tsarkake wannan bangare na sharia a gwamnatin - Abubakar Tsav ga sabon Cif Jastis

Ka tsarkake wannan bangare na sharia a gwamnatin - Abubakar Tsav ga sabon Cif Jastis
Source: UGC

Tsohon kwamishinan yan sanda na jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsav ya shawarci mukaddashin alkalin alkalan Najeriya, Mai shari'a Tanko Mohammed da ya kawo gyara da zai tsaftace bangaren shari'a na kasar nan.

Wannan na kunshe ne a takardar da yasa hannu kuma ya mika ga manema labarai a ranar asabar a garin Makurdi.

Tsav yace akwai bukatar sabon alkalin alkalan da ya kawo gyare gyare da zasu tsaftace bangaren.

"Akwai bukatar Mohammed da ya duba irin abubuwan da suka sa har aka zabe shi ya zamo matashiya wajen kawo gyara kuma tare da fada da rashawa don tsaftace bangaren," yace.

Yayi jajen cewa yanke shawarar Buhari na dakatar da Onnoghen an maida abin siyasa da kabilanci ga wasu yan Najeriya a maimakon su maida hankali wajen duban laifin da ya kawo dakatarwar.

"Bangaren shari'a a Najeriya ta kai halin da ake bukatar gyara sakamakon tsananin barnar da akayi. Matakin da shugaban kasa ya dauka yayi daidai kuma na cigaba ne tare da farfado da nagartar bangaren."

"Amma abin mamaki shine yanda aka duba matakin ta bangaren siyasa da kabilanci."

"Musun da masu bin bayan Onnoghen keep taso dashi don kare shi suna kara dakushe nagartar alkalin tare domin yanda yan siyasa suka tashi don kare shi," inji Tsav.

GA WANNAN: Rigimar ta koma Majalisa, bayan da Buhari ya aika kudurin N30,000 na ma'aikata ga majalisu

Tsohon kwamishinan gwamnatin tarayya na ofishin korafe korafe na jama'a ya jinjinawa shugaban kasar akan matakin da ya dauka kuma ya hori tsohon alkalin alkalan da ya je gaban kotun don wanke sunan shi akan laifin da ake zargin shi.

"Doka tana kan kowa, don haka Onnoghen ya bayyana kawai don nunawa yan Najeriya cewa ya yarda da hukunce hukuncen da ya dinga yanke musu a shekarun da suka gabata. Duk da shima ya yarda da ya aikata laifi. Yanzu ya rage mishi da yaje ya kare kanshi akan laifin da ya aikata."

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa a ranara juma'a Buhari ya dakatar da Onnoghen akan kin bayyana kadarorin shi kuma ya rantsar da mai shari'a Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel