Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau

Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau

- Canzawar alkiblar jam'iyyar ACPN yasa na janye

- Yan Najeriya na bukatar shuwagabanni masu kishin kasa

- Ta karyata zargin da shugaban jam'iyyar ACPN ya bayyana

Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau

Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau
Source: Facebook

Obiageli Ezekwesili, yar takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar ACPN, tace canzawar alkibla da manufofin jam'iyyar suka sa ta janye daga takarar shugabancin kasa.

Ezekwesili ta sanar da janyewar ta daga takarar ne a ranar talata.

Tace aiyukan jam'iyyar ne tasa ta janye.

Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau

Nayi matukar kuskure da na dauka ACPN na da akida mai kyau
Source: UGC

Abdul-Ganiyu Galladima, shugaban jam'iyyar ta kasa ya zargi Ekwesili da rashin maida hankali a jam'iyyar. Ya zargi tsohuwar ministan ta shiga jerin manema matsayin ministan kudi.

Biyo bayan hakan, Jam'iyyar ta goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari don zarcewa mulkin kasar.

Da tayi magana akan matsalar tace: "Naji dadin karanta martanin da yan kishin kasa sukayi akan yanke shawarar janyewa daga takarar tare da barin jam'iyyar ACPN. Naga kuma yanda shuwagabannin ACPN sukayi da suka ji matsayata," inji takardar

"Abin dadi kuma shine, sun taimaka ta yanda suka bayyanawa mutane dalilina na barin tsakanin su. Ya za'ayi bayan na gane canjin manufofi na Shuwagabannin jam'iyyar in cigaba da zama a jam'iyyar? Manufata shine in samu yan kasa da zamu canza tsofafin siyasar APCPDP. Najeriya da yan Najeriya sun cancanci sababin yanayin siyasa da kuma shuwagabanni da zasu iya mulki wanda nayi kuskuren cewa suna tare da ACPN, amma sai suka nuna min ba hakan bane."

GA WANNAN: An fara bincikar tsohon IGP kan N322m ta zabukan bana da suka yi batan dabo

"Canza manufofin jam'iyyar ce tasa nayi saurin janyewa daga takarar da na tsaya don in taimaka wajen gina gwamnati mai aminci. A don haka ne a take na sadaukar da takarata don in cigaba da rike martaba ta."

"Yanke shawarar su goyi bayan dan takarar APC wanda mataimakina a da ya sanar kuma shugaban jam'iyyar ACPN ya bayyana siyasar su ta dogaro da kai wanda suka nunawa yan Najeriya. Umarni ne."

Ezekwesili ta karyata zargin da shugaban jam'iyyar yake mata, ta kwatanta su da 'karya kirkirarra'.

Akan zantukan bata sunap da ake a kaina daga shuwagabannin ACPN, inaso yan Najeriya su gane cewa babu burbushin gaskiya a cikin su," inji ta.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel