Yanzu Yanzu: APC ta yi babban rashi yayinda tsohon Gwamna Nwobodo ya koma PDP

Yanzu Yanzu: APC ta yi babban rashi yayinda tsohon Gwamna Nwobodo ya koma PDP

- APC ta yi babban rashi a yankin kudu maso gabas gabannin zaben kasar mai zuwa

- Tsohon gwamnan toshuwar jihar Anambra, Sanata Jim Nwobodo ya sauya sheka zauwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP

- Kungiyar Ohanaeze ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin kudu maso gabas ta yi babban rashi a kokarinta na kwace yankin yayinda tsohon gwamnan toshuwar jihar Anambra, Sanata Jim Nwobodo ya sauya sheka zauwa tsohuwar jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP), jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: APC ta yi babban rashi yayinda tsohon Gwamna Nwobodo ya koma PDP

Yanzu Yanzu: APC ta yi babban rashi yayinda tsohon Gwamna Nwobodo ya koma PDP
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa a wajen taron sauya shekar da aka gudanar a gidansa, tsohon ministan harkokin waje, Cif Dubem Onyia, ya fada ma tsohon gwamnan cewa suna a gidansa ne don neman ya dawo ga iyalansa wato PDP, inda mutanensa suka samu damar dawo da Ndigbo.

A halin da ake ciki, mun ji cewa babbar kungiyar Inyamuran Najeriya wanda ke kare muradin duk wani dan kabilar ibo a Najeriya da ma duniya gaba daya, Ohanaeze ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar jam’iyyar PDP a matakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu yarda da ganin shugaba mara lafiya ba – Kungiyoyin jama’a ga Buhari

Legit.ng ta ruwaito shugaban Ohanaeze, John Nwodo ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu a garin Enugu, bayan wata doguwar tattaunawa da kungiyar ta yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel