Ba za mu yarda da ganin shugaba mara lafiya ba – Kungiyoyin jama’a ga Buhari

Ba za mu yarda da ganin shugaba mara lafiya ba – Kungiyoyin jama’a ga Buhari

- Wasu kungiyoyin jama’a sun yi kira ga shugaban kasa Buhar da ya kaddamar da matsayin lafiyarsa kafin zaben 2019

- Kungiyoyin sun bukaci hakan ne yayinda suke wani tattaki a jihar Lagas a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu

- Shugaban kungiyar Equity and Justice Movement, daya daga cin kungiyoyin yace kasar ba za ta iya amincewa da shugaba mara lafiya kuma wanda ba zai iya shugabanci ba

Wasu gamayyar kungiyoyin jama’a 12 sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhar da ya kaddamar da matsayin lafiyarsa kafin zaben 2019. Kungiyoyin sun bukaci hakan ne yayinda suke wani tattaki a jihar Lagas a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu.

Obatungashe Adebayo, shugaban kungiyar Equity and Justice Movement, daya daga cin kungiyoyin yace kasar ba za ta iya amincewa da shugaba mara lafiya kuma wanda ba zai iya shugabanci ba.

Ba za mu yarda da ganin shugaba mara lafiya ba – Kungiyoyin jama’a ga Buhari

Ba za mu yarda da ganin shugaba mara lafiya ba – Kungiyoyin jama’a ga Buhari
Source: UGC

Yace: “Muna son shugaban kasa da kansa ko likitan say a fito ya fada mana matsayar lafiyarsa domin tabbatar da cewa shugaban kasar na da lafiya, kuma zai iya mulkar kasar a shekaru hudu masu zuwa idan mutane suka zabe sa.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar Buhari: NSCDC ta tsaurara matakan tsaro a jihar Oyo

“Muna son shi; bama adawa da shi. Abunda muke fadi shine cewa una son sa kamar yadda uke son kasar nan sannankua muna masu ruwa da tsaki a ajandar ci gaban kasar nan.

“Ba za mu iya hakura da ganin wani shugaba da baida lafiya sannan bai da kuzarin mulkar kasar ba yadda ya kamata domin kawo ci gaba kamar yadda aka shirya.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel