Fayose ya tafi ya bar mani bashin sama da Biliyan 150 – Gwamnan Ekiti

Fayose ya tafi ya bar mani bashin sama da Biliyan 150 – Gwamnan Ekiti

- Kayode Fayemi na Jihar Ekiti yace Ayodele Fayose ya bar masa bashi

- Gwamnan na Ekiti yace ya gaji bashin Biliyan 155 daga hannun Fayose

- Tsohon Gwamnan Jihar Fayose yayi watsi da zargin da Fayemi yake yi

Fayose ya tafi ya bar mani bashin sama da Biliyan 150 – Gwamnan Ekiti

Gwamnan Ekiti Fayemi ya koka da halin da ya karbi Jihar
Source: UGC

Gwamnan jihar Ekiti watau Dr Kayode Fayemi ya zargi tsohon gwamna Mista Ayodele Peter Fayose da barin masa jihar da tarin bashin kudi. Kayode Fayemi yayi kaca-kaca da gwamnatin Fayose wanda yace ta kuntatawa mutanen Ekiti.

A Ranar Alhamis ne Kayode Fayemi yayi jawabi bayan cikar gwamnatin sa kwana 100 a kan karagar mulki. Fayemi wanda yayi amfani da wanda dama wajen sa hannu a kan kasafin kudin jihar na bana yace Fayose ya hada sa da aiki.

Gwamnan mai-ci ya bayyanawa manema labarai cewa ya gaji bashin makudan bashi da aka ci a gida da kasar waje daga hannun gwamnatin baya. Daga cikin wannan bashi akwai tarin albashin Ma’aikata da ke kan wuyan gwamnatin jihar.

KU KARANTA: 2019: Fayose ya jaddada goyon bayan sa ‘Dan takarar PDP Atiku

Fayemi yace Fayose ya bar mulki ana bin jihar Ekiti albashin Ma’aikata na sama da Biliyan 16. Akwai kuma bashin da ake bin jihar wanda ya kusa kai Biliyan 60. Bugu da kari kuma kudin fansho na tsofaffin Ma’aikata na akalla Biliyan 39.

Bayan wannan kuma gwamnan yace akwai alawus din Ma’aikata da masu bautar kasa a Ekiti wanda ya haura Naira Biliyan 4 a kan sa. Akwai kuma kudin ‘yan kwangila na sama da Biliyan 28 da kuma wasu haraji da ake bin jihar da dai sauran su.

Tuni dai tsohon gwamna Ayodele Fayose yayi watsi da wannan zargi inda yace gwamna Kayode Fayemi bai yi wani abin kwarai da za a zo a gani a cikin kwanaki 100 da yayi yana jan ragamar jihar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel