Yan Nigeria ba zasu gane sun yi kuskure ba sai sun sake zabar Buhari da APC a 2019 - Falae

Yan Nigeria ba zasu gane sun yi kuskure ba sai sun sake zabar Buhari da APC a 2019 - Falae

- Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Chief Olu Falae, ya ce 'yan Nigeria na cikin mawuyacin hali na bukatar shugaba adali

- Ya ce ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen dakatar da shugaban kasa Buhari a kudurinsa na samun nasarar zarce a zabe mai zuwa

- A nashi jawabin, Fasoranti ya bayar da tabbacin cewa kungiyar Afenifere zata goyi bayan dan takarar da zai sake fasalin Nigeria

Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Chief Olu Falae, ya ce 'yan Nigeria na cikin mawuyacin hali na bukatar shugaba adali. Ya ce ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kudurinsa na samun nasarar zarce a zaben ranar 16 ga watan Fabreru da ke gabatowa.

Falae, wanda kuma shine tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan a lokacin da uwar gidan dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Mrs Titi Abubakar ta ziyarci shuwagabanin kungiyar bunkasa al'ummar Yoruba, Afenifere, a gidan Reuben Fasoranti da ke Akure, jihar Ondo.

Ya ce: "Ya zama wajibi mu dakatar da wannan gwamnati mai ci a yanzu daga komawa saman mulki, saboda mu kanmu, da kuma shi kansa Buhari. Sam bai san abubuwan da ke faruwa a kasar ba. Bana tunanin yana da cikakkar lafiya. Ya kamata ya je gidane kawai ya huta. Akwai masu dukan jaki suna dukan taiki.

KARANTA WANNAN: Saboda Buhari, zan iya rike mukamin shugaban karamar hukuma - Tsohon gwamnan Bauchi

Yan Nigeria ba zasu gane sun yi kuskure ba sai sun sake zabar Buhari da APC a 2019 - Falae

Yan Nigeria ba zasu gane sun yi kuskure ba sai sun sake zabar Buhari da APC a 2019 - Falae
Source: Depositphotos

"Ina yiwa Atiku fatan alkairi. Muna akan turba daya ne, muna jifar tsuntsu daya ne. Babu wanda ke son wannan gwamnati ta ci gaba da mulki saboda ta yaudaremu. Abubuwa da dama da a baya ba a yinsu, yanzu an dawo ana yinsu, rikicin makiyaya, garkuwa da mutane kamar wasu kaji.

"Ya zama wajibi mu hada karfi da karfe wajen cimma sakamako daya. Ina baku tabbacin cewa muna kan turba daya, muna nemawa kasarmu 'yanci daga wannan irin mulkin kama karyar. Mulkin da ya jefa kowa cikin bala'i, tsoro da tashin hankali, kuma ya zama wajibi mu kawo karshensa."

A nashi jawabin, Fasoranti ya bayar da tabbacin cewa kungiyar Afenifere zata goyi bayan dan takarar da zai sake fasalin Nigeria.

A nata bangaren, uwar gidan Atiku Abubakar, Mrs Titi, ta baiwa kungiyar tabbacin cewa mijin nata ya sha alwashin sake fasalin kasar, kuma zai yi aiki kafada da kafada da al'ummar Yoruba a kasar

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel