Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma

Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma

- Kwararru a diplomasiyya sun tabbatar da zasu tallafa wajen tabbatar da zabe mai inganci a Najeriya

- Babbar kwamishinan Birtaniya ta ja kunnen yan siyasa da su guji karya dokokin zabe

- Kwamishinan Birtaniya da mukaddashin sifeta janar sun gana akan tsaro

Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma

Duk wanda ya sake murdiyya a zabe, zai fuskanci takunkumai daga Turawan Yamma
Source: Getty Images

Kwararru a diplomasiyya sun tabbatar da zasu goyi bayan kungiyar yan sandan turai da sauran yan diplomasiyyar kasashen duniya sun tabbatar wa yan sandan Najeriya cewa zasu tallafa musu a zabe mai zuwa.

Shugaban wakilan da kuma babban kwamishinan Birtaniya, Catriona Laing sun bada tabbaci a yayin taron da sukayi da mukaddashin sifeta janar na yan sandan Najeriya a hedkwatar jami'an tsaro dake Abuja.

GA WANNAN: Nan da mako daya kacal zamu iyar da karancin Albashi don talakka ya samu kafin ya jefa kuri'a

Catriona tace akwai tsari mai kyau da jami'an yan sanda suka shirya don tabbatar da zabe mai yanci da inganci.

Ta kara jan kunnen yan siyasa akan taka dokar zabe saboda zasu iya fuskantar hukunci akan haka.

Kamar yanda aka sani zaben 2019 na gabatowa don haka cibiyoyin tsari ke ta shirye shiryen tabbatar da zabe na yanci da inganci.

Shirye shiryen ne ke jawo jami'ai wadanda zasu lura da yanayin zaben don tabbatar da ingancin shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel