Kamfen din Atiku: ‘Yan daba sun hallaka wani bawan Allah a Kaduna

Kamfen din Atiku: ‘Yan daba sun hallaka wani bawan Allah a Kaduna

- Yan daba sun kai farmaki tare da hallaka wani bawan Allah bayan kammala taron Atiku a Kaduna

- A jiya ne Atiku ya gudanar da yakin neman zabensa a jihar Kaduna

- Marigayin ya hadu da ajalin sa ne bayan wasu Matasa su shida dauke da wukake suka bi shi gefen filin wasan Ahmadu Bello

Wasu gungun Matasa ‘yan sara suka dauke da Muggan makamai sun kashe wani Bawan Allah mai suna Kabiru Kantoma, bayan kammala taron Atiku a garin Kaduna Jiya.

Marigayin ya hadu da ajalin sa ne bayan wasu Matasa su shida dauke da wukake suka bi shi gefen filin wasan Ahmadu Bello, wurin da aka yi taron, suka yi ta burma masa wuka har sai da ya fadi kasa warwas.

Kamfen din Atiku: ‘Yan daba sun hallaka wani bawan Allah a Kaduna

Kamfen din Atiku: ‘Yan daba sun hallaka wani bawan Allah a Kaduna
Source: Depositphotos

A cewar maiyarmu an wuce da Kabiru wani asibiti domin yi masa magani amma daga bisani yace ga garin ku nan.

An tattaro cewa mutanen sun tsere daga wurin suna ganin Kabiru ya fadi kasa jina jina.

KU KARANTA KUMA: Sama da yan PDP da ADP 2,500 ne suka sauya sheka zuwa APC a Edo

A baya mun ji cewa dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yiwa al'ummar Najeriya sabon alkawali da zai cika muddin ya cimma nasara a zaben watan gobe.

Yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar yake kyautata zaton samun nasara da goyon bayan al'ummar kasar nan a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe, ya sha alwashin dawowa da Najeriya dukkanin wata martaba da arziki da suka tsere ma ta a karkashin jagoranci na jam'iyyar mai ci ta APC.

Furucin Atiku ya biyo bayan ikirarin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza daukar nauyin kasar nan wajen jagorantar kimanin mutane miliyan 200 da ta kunsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel