Babbar magana: An cafke mataimakin kwamishinan 'yan sanda na bogi, hoto

Babbar magana: An cafke mataimakin kwamishinan 'yan sanda na bogi, hoto

- 'Yan sanda sunyi nasarar kama wani Kingsley Udoyen da ke yin sojan gona a matsayayin mataimakin kwamishinan 'yan sanda (ACP) a Akwa Ibom

- Kingsley Udoyen ya amsa aikata laifin kuma da aka bincika gidansa an gano bindiga, manyan hotunan 'yan sanda, kayan 'yan sanda, katin shaida bogi da sauransu

- Rundunar 'yan sandan ta kuma yi hole wasu mutane 213 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da kisa, garkuwa da mutane, fyade da sauransu

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Akwa Ibom tayi holen wani Kingsley Udoyen da aka kama yana yin sojan gona a matsayin mataimakin kwamishinan yan sanda wato ACP.

Anyi holen sa ne tare da wasu da ake zargi da aikata laifuba daban-daban su 213 a ranar Alhamis. Ana tuhumarsu ne da aikata laifuka da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, satar yara, fyade da fashi da makami. An aikata laifukan ne a cikin Janairun 2019.

An kama mataimakin kwamishinan 'yan sanda na bogi

An kama mataimakin kwamishinan 'yan sanda na bogi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Goyon bayan Buhari ya yi sanadiyar mutuwar aure

A yayin da ya yiwa manema labarai bayani, Kwamishinan yan sandan jihar, Musa Kimo ya ce sojan gonar ya yi amfani da damar domin barazana da damfarar mutane da dama.

A cewar Kimo, an kama Kingsley Udoyen da ke zaune a Stadium Road, Abak ne a ranar 2 ga watan Janairun 2019 saboda laifin yin sojan gona a matsayin babban jami'in dan sanda mai mukamin mataimakin kwamishina (ACP) inda ya rika damfarar mutane da yi musu barazana.

"Da aka bincika gidansa, an gano bindigan hannu babu harsashi, manyan hotunan Sufritandan 'yan sanda da na mataimakin kwamishinan 'yan sanda, kayan 'yan sanda uku, damarar 'yan sanda, katin shaida na bogi da wasu takardu," inji Kimo.

Kazalika, an kuma kama mutane 213 da ake zargi da aikata wasu laifuka, a cikinsu, an gurfanar da 111 a kotu. Sauran kuma ana cigaba da gudanar da bincike a kansu, an saki wadanda ba a same su da laifi ba.

Ana zarginsu da aikata laifuka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, satar yara, fyade da fashi da makami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel