Gwamnatin Anambara tace babu ita a kiran da a zabi Atiku da PDP

Gwamnatin Anambara tace babu ita a kiran da a zabi Atiku da PDP

- Gwamnatin jihar Anambra ta wanke kanta daga takardar da Ohanaeze Ndigbo ta mika na goyon bayan Atiku

- Gwamnatin jihar tace Ohanaeze Ndigbo bishiya ce da kowanne inyamuri zai sha inuwar ta

- Abin dana sani ne ace kungiyar da ta kunshi yan jam'iyya daban daban ta goyi bayan wani bangare

Gwamnatin Anambara tace babu ita a kiran da a zabi Atiku da PDP

Gwamnatin Anambara tace babu ita a kiran da a zabi Atiku da PDP
Source: UGC

Gwamnatin jihar Anambra ta wanke kanta daga takardar da kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bada na goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar a zaben shugabancin kasa na 16 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Abubakar Dan takarar shugabancin kasa ne karkashin jam'iyyar PDP.

Farfesa Solo Chukwulobelu, sakataren gwamnatin jihar Anambra ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar Enugu.

Chukwulobelu ya bayyana cewa abinda takardar ta kunsa baya cikin matsayar gwamnatin Anambra.

Idan za a tuna wani bangare na Ohanaeze Ndigbo 'Ime Obi' a taron ranar alhamis a Enugu sun bayyana suna bayan Abubakar.

Ime Obi kamar bangare ne na maida martanin gaggawa na Ohanaeze Ndigbo da suka kunshi wakilai daga jihohi 7 da suka hada kungiyar wacce ta kunshi gwamnonin jihar.

Chukwulobelu ya nuna mamakin shi ta yanda babbar kungiyar inyamuran ta yanke hukuncin bin bayan wani bayan kuma kungiyar ta kunshi yan jam'iyyu daban daban.

GA WANNAN: Akwai manyan kalubale kan tsaro a lokacin zabuka, amma kuma duk zamu shawo kansu - DSS

Chukwulobelu yace,"Mun karanta kadan daga cikin abinda takardar ta kunsa wacce shuwagabannin Ohanaeze suka bada. Munyi dana sanin cewa basu kunshi matsayar mutane da gwamnatin jihar Anambra ba.

Matsayar gwamnatin jihar Anambra shin Ohanaeze ta zama bishiya wacce duk inyamurai zasu mori inuwar ta, kuma kada ta dau wani bangare na kowacce jam'iyyar siyasa. Akwai manyan shuwagabanni a duk jam'iyyun siyasa a cikin ta. Abin dana sani ne ace kungiyar ta goyi bayan wani bangare da zai iya kawo rashin hadin kan inyamurai na shekaru da dama ba," inji shi.

Sakataren jihar yace Gwamna Willie Obiano yatura wakili don halartar taron da ya kira kungiyar a Enugu.

"Wakilin mu ya isa da wuri don taron za ayi shi ne 7 na yamma a ranar alhamis. Amma abin mamaki shine har anyi taron da wuri wanda minti 30 kacal ya dauka."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel