An fara bincikar tsohon IGP kan N322m ta zabukan bana da suka yi batan dabo

An fara bincikar tsohon IGP kan N322m ta zabukan bana da suka yi batan dabo

Mukaddashin sifeta Janar na yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a ranar alhamis ya bukaci yan kungiyar da tsohon sifeta Janar Ibrahim Idris ya hada don zabe dasu yi bayani akan yanda suka raba Naira Miliyan 311.649 da aka ba kwamitin.

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya
Source: Facebook

Mukaddashin sifeta Janar na yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a ranar alhamis ya bukaci yan kungiyar da tsohon sifeta Janar Ibrahim Idris ya hada don zabe dasu yi bayani akan yanda suka raba Naira Miliyan 311.649 da aka ba kwamitin.

Majiyar mu ta hedkwatar jami'an tsaro tace an kira wasu yan kwamitin sun kuma amsa tambayayi sannan suka koma guraren aiyukan su.

Majiyar tamu bata bayyana mana yan kwamitin guda nawa suka amsa kiran ba da matsayin su.

Sifeta janar din ya ba DIG Mohammed Katsina umarnin musu tambayoyi.

Amma wata majiyar tamu mai karfi tace chiyaman din kwamitin wanda kwamishinan yan sanda ne bai amsa kiran ba saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara yankin shi. Har yanzu dai bamu ji dalla dallar tambayoyin da akayi musu ba.

GA WANNAN: INEC ta kuma yin warwatsi da wani dan takarar APC bayan na jihar Ribas

Binciken majiyar mu ya gano cewa tsohon sifeta janar na yan sanda ya rubuta wasika game Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Disamba 2018 da bukatar kudin.

Majiya mai kyau tace an bawa kwamitin kudin da suka bukata.

Idris yasa wa kwamitin suna' Binciken barazanar kafin zabe da kuma dabarun tsaro na magance su'.

Kwamitin ya samu shugabancin kwamishinan yan sanda da wasu kwamishinoni yan sanda biyu tare da mataimakan kwamishinoni uku.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel