2019: Kuri’a ta tana wajen Atiku da Obi inji tsohon Gwamna Fayose

2019: Kuri’a ta tana wajen Atiku da Obi inji tsohon Gwamna Fayose

- Tsohon Gwamna Ayodele Fayose yace Atiku ne zabin sa a zaben 2019

- Fayose ya sa kayan Hausawa na babbar riga da na Ibo yana yin kamfe

2019: Kuri’a ta tana wajen Atiku da Obi inji tsohon Gwamna Fayose

Fayose yace #ShugabanNajeriya sai Atiku da Obi
Source: Instagram

Mun ji labari cewa tsohon Gwamnan jihar Ekiti watau Mista Ayodele Peter wanda ya bar gadon mulki a bara ya jadadda goyon bayan sa a zaben da za ayi kwanan nan ga ‘dan takarar jam’iyyar adawar PDP watau Alhaji Atiku Abubakar.

Tsohon gwamnan na PDP zai marawa Atiku Abubakar baya ne domin ganin ya tika shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa a zaben Najeriya. Yanzu dai saura kusan makonni 3 rak ne su ka rage a gudanar da babban zaben kasar.

KU KARANTA: Inyamuran Jihar Kano sun ce za su zabi Ganduje a 2019

2019: Kuri’a ta tana wajen Atiku da Obi inji tsohon Gwamna Fayose

Fayose cikin kayan Ibo yana yi wa Atiku da Obi kamfe
Source: Facebook

Ayo Fayose ya tabbatar da cewa kuri’ar sa ta Atiku Abubakar ce a shafin sa na Tuwita inda ya sanya hotunan sa har 2. An ga tsohon gwamnan sanye da kayan Hausawa na babbar riga da kuma hular mutanen Arewa ta Zanna-Bukar.

Fayose ya kuma ci rigar Ibo da ‘yar jar hula inda yayi jawabi da Turanci cewa kuri’ar sa tana wajen Atiku Abubakar da Peter Obi na PDP domin ganin an gyara kasar. Dama Fayose yana cikin manyan masu sukar gwamnatin APC.

Ayo Fayose yayi yunkurin yin takarar shugaban kasa bana a PDP, sai dai daga baya ya janye kafin a kai ga zaben fitar da gwani. Wannan ya sa jam’iyyar ta yaba masa inda aka bar ‘Yan Arewa su ka gwabza.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel