Kotu ta maida wa Donald Duke takarar sa ta kujerar shugaban kasa

Kotu ta maida wa Donald Duke takarar sa ta kujerar shugaban kasa

- Kotun daukaka kara ta kwace takarar kujerar shugaban kasa ta jam'iyyar SDP daga hannun tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana

- Mai shari'a Abdu Aboki, shine ya jagoranci zaman kotun tare da zartar da hukuncin mai sanyaya zuciyar wakilan jam'iyyar

- Kotun ta mayar da takarar jam'iyyar ga tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke

A yau Alhamis, 24 ga watan Janairu, 2019, kotun daukaka kara dake garin Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun tarayya wadda a baya ta tabbatar da Farfesa Jerry Gana a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar SDP (Social Democratic Party).

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, kotun daukaka kare da ke zaman ta cikin garin Abuja a yau Alhamis ta kwace takarar kujerar shugaban kasa ta jam'iyyar SDP daga hannun tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana.

Tsohon Gwamnan jihar Cross River; Donald Duke
Tsohon Gwamnan jihar Cross River; Donald Duke
Source: Facebook

Yayin zaman kotun da ta gudanar a yau bisa jagorancin Alkalin ta, Mai shari'a Abdu Aboki, ta mayar da takarar jam'iyyar ga tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Ko shakka ba bu jam'iyyar SDP bayan kammala zaben ta na fidda gwani da ta gudanar a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, ta tabbatar da nasarar Donald Duke, wanda ya lashe kuri'un wakilai 812 yayin da Farfesa Gana ya samu kuri'u 611 kacal.

KARANTA KUMA: Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa, ta riga mu gidan gaskiya

Duba da yadda kundin tsari na jam'iyyar ya haramta fidda dan takarar kujerar shugaban kasa wanda ya fito daga shiya daya ta Najeriya tare da shugaban jam'iyyar, ya sanya wata babbar kotun tarayya ta kwace takarar Donald a watan Dasumba na bara.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a jiya hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayar da shaidar cewa kawowa yanzu ba ta aminta da kowane dan takara ba na jam'iyyar SDP da zai rike ma ta tuta a yayin babban zabe da za a gudanar cikin watan gobe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel