Boko Haram: Cacar baki ta kacame tsakanin Buhari da jam'iyyar PDP

Boko Haram: Cacar baki ta kacame tsakanin Buhari da jam'iyyar PDP

Kimanin 'yan kwanaki kadan da tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tare da ikirarin cewa gwamnatin tarayya a yanzu ta yi wa harkar tsaro rikon sakainar kashi, Buhari ya karyata hakan.

Da yake yiwa dubban magoya bayan sa jawabi a filin wasa na Giginya a jihar Sokoto yayin gangamin yakin neman zaben sa, Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samar da tsaro ingantacce a jahohin Yobe da Borno.

Boko Haram: Cacar baki ta kacame tsakanin Buhari da jam'iyyar PDP

Boko Haram: Cacar baki ta kacame tsakanin Buhari da jam'iyyar PDP
Source: UGC

KU KARANTA: Sojoji sun kubutar da mutane 61 daga hannun 'yan Boko Haram

Legit.ng Hausa ta samu cewa su kuwa jam'iyyar PDP ta kasa a nata martanin ga ikirarin na shugaban kasa, cewa ta yi labarin kanzon kurege ne kawai domin kuwa kungiyar Boko Haram har yanzu tana cin karen ta ba babbaka.

A wani labarin kuma, Kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya, Honorabul Yakubu Dogara ya bayyana dalilin su da yasa suke adawa da tazarcen shugaban kasa Muhammau Buhari a zaben dake tafe nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa.

Yakubu Dogara ya bayyana cewa ba wai suna adawa da Buhari don basu sonshi a kashin kansu ba ne, illa kawai domin tabbatar da samar da Najeriya makoma mai kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel