Babbar magana: APC ta sanya kyauta mai tsoka ga akwatin da yafi tarawa Buhari kuri'u a Filato

Babbar magana: APC ta sanya kyauta mai tsoka ga akwatin da yafi tarawa Buhari kuri'u a Filato

- Manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, sun sha alwashin bayar da kyauta mai tsoka ga duk wani akwatin zabe da ya tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a zaben 2019

- Shugaban karamar hukumar Jos ta Kudu, Mr Gideon Davou, ya bayyana hakan a yayin kaddamar da yakin zaben gida-gida na jam'iyyar APC a Filato

- Davou ya jaddada cewa jam'iyyar PDP bata da wani gurbi a Jos ta Kudu, yana mai cewa karamar hukumar ta APC ce zalla tun bayan kammala zaben 2015

Manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Filato, sun sha alwashin bayar da kyauta mai tsoka ga duk wani akwatin zabe da ya tarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Simon Lalong dama sauran 'yan takara karkashin APC, kuri'u mafi yawa a zaben 2019.

Shugaban masu ruwa da tsakin kuma shugaban karamar hukumar Jos ta Kudu, Mr Gideon Davou, ya bayyana hakan a yayin kaddamar da yakin zaben gida-gida na jam'iyyar APC a Filato, jihar Jos.

Ya ce shiyyar mazabar Arewacin jihar sun yanke shawarar ci gaba da rikon turbar nan ta karba karba da marigayi Chief Solomon Lar ya assasa wacce ta baiwa kowacce shiyyar mazaba damar fito da dan takarar kujerar gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Yadda Babangida ya kitsa makircin raba kan Obasanjo da Atiku

Babbar magana: APC ta sanya kyauta mai tsoka ga akwatin da yafi tarawa Buhari kuri'u a Filato

Babbar magana: APC ta sanya kyauta mai tsoka ga akwatin da yafi tarawa Buhari kuri'u a Filato
Source: Twitter

Ya ce al'ummar shiyyar Kudancin mazabar jihar sun ki amincewa da mataimakin gwamna, Dame Pauline Tallen a 2011 inda suka fito kwansu da kwarkwatarsu wajen zabar Sanata Jonah Jang a matsayin gwamna, yana mai cewa yanzu lokaci yayi da ya kamata a sake zabar Lalong a karo na biyu.

Davou ya ce idan har al'ummar yankin suka zabi Jeremiah Useni ko wani dan takara daga jam'iyyar adawa, to kuwa zai wargaza wannan tsari na karba karba ta shiyyoyin zaben jihar, yana mai cewa duk wani sabon dan takara da ya samu nasara zai bukaci sake zarcewa a 2023, wanda kuma ya sabawa tsarin shiyyoyin.

Ya sha alwashin jagorantar gangamin yakin zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamna Lalong da kuma dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.

Davou ya jaddada cewa jam'iyyar PDP bata da wani gurbi a Jos ta Kudu, yana mai cewa karamar hukumar ta APC ce zalla tun bayan kammala zaben 2015.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel