Asiri ya tonu: Yadda Babangida ya kitsa makircin raba kan Obasanjo da Atiku

Asiri ya tonu: Yadda Babangida ya kitsa makircin raba kan Obasanjo da Atiku

- Theophilus Danjuma, ya ce Ibrahim Babangida, ya kitsa makirci domin gwara kan shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abubakar

- Mr Danjuma ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba, 2002 da jakan Amurka a Nigeria na wancan lokacin, Howard Jeter, a Abuja

- Amma a wannan gabar, shekarar 2018 ta zo da wani sabon salo, inda Mr Obasanjo ya yafewa Mr Atiku dukkanin wasu laifuka da ya aikata masa

Wani tsohon hafsan rundunar sojin kasa, Theophilus Danjuma, ya ce tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Ibrahim Babangida, ya kitsa makirci domin gwara kan shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abubakar, domin haddasa gaba a tsakaninsu, tun ma a gwamnatinsa ta farko daga 1999 zuwa 2003.

Mr Danjuma ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba, 2002 da jakan Amurka a Nigeria na wancan lokacin, Howard Jeter, a Abuja. Kafar watsa labarai ta Wikileaks ta watsa hirar a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2002.

A yayin wannan taron, 'yan siyasa sun gurbata dangantakar da ke tsakanin Mr Obasanjo da Mr Abubakar, musamman ganin cewa zaben 2003 na karatowa a lokacin, kuma Mr Obasanjo na fuskantar barazanar tsigewa daga 'yan majalisun tarayya, bisa jagorancin Ghali Na'Abba.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Babbar kotun gwamnatin tarayya ta canjawa alkalai wajen aiki

Asiri ya tonu: Yadda Babangida ya kitsa makircin raba kan Obasanjo da Atiku

Asiri ya tonu: Yadda Babangida ya kitsa makircin raba kan Obasanjo da Atiku
Source: UGC

A cewar kafar watsa labarai ta The Cable, ta hanyar kafa hujja da dakin karatun jama'a na diplomasiyar Amurka, Mr Danjuma, wanda a lokacin yake matsayin ministan tsaro, ya ce Mr Babangida ya dade yana kitsa makircin gwara kan Obsanjo da Atiku da kuma burin son ganin sun dawo a tafin hannunsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Mr Babangida ya fara yunkurin jan ra'ayin Mr Obasanjo na rabuwa da Mr Abubakar domin kare martabar shi Obasanjon, musamman a Arewacin Nigeria. A cewar Mr Danjuma, bayan shafe watanni 9 ba tare da Mr Babangida ya samu nasara ba, sai kuma ya koma bangaren Atiku.

A tsaka da wannan tata-burza da ake yi tsakanin Obasanjo da Atiku, a daren ranar da Mr Abubakar ke jagorantar taron kasa na jam'iyyar PDP a Abuja, ya ce har yanzu manufarsa a bude take. In ma dai ya kalubalanci Mr Obasanjo a neman takara, ko yin takara tare da shi ko kuma yin takara tare da wani dan takara (wanda ba zai wuce Alex Ekwueme ba wanda shine yafi kowa tagomashi a masu sha'awar takara a taron.)

Sai dai, Mr Obasanjo ya canja labarin, inda ya ce zai ci gaba da tafiya da Mr Abubakar a matsayin mataimakinsa idan har an sake bashi damar tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar.

Sai dai gabarsu ta sake ruruwa a lokacin da Mr Obasanjo ya gaji da Mr Abubakar, da kuma yadda yake gudanar da sha'anin shugabancin kujerarsa, inda ya koreshi daga PDP kafin zaben 2007. A lokacin ne kuma Obasanjo ya dawo mai cikakken iko da jam'iyyar da shuwagabanninta, wanda har ya gabatar da bukatar sake fasalin kundin mulkin kasar domin bashi damar yin shugabanci har a karo na ukku.

Sai dai wannan yunkuri na sa ya tashi a banza, bayan da majalisar dattijai taki amincewa da sake fasalin dokar mulkin kasar, wannan ne kuma ya sa Mr Obasanjo ya dauko gwamnan jihar Katsina Umaru Musa Yar'Adua, a matsayin dan takarar shugaban kasar karkashin PDP, wanda kuma ya rasu a 2010, bayan fama da rashin lafiya.

Amma a wannan gabar, shekarar 2018 ta zo da wani sabon salo, inda Mr Obasanjo ya yafewa Mr Atiku dukkanin wasu laifuka da ya aikata masa, tare da kuma bayyana shi a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin PDP a garin Fatakwal, a lokacin zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel