Akwai matsala idan Atiku ya zama shugaban kasar Najeriya - inji kungiyar fulani

Akwai matsala idan Atiku ya zama shugaban kasar Najeriya - inji kungiyar fulani

Babbar kungiyar nan dake fafutukar kare muradun 'yan kabilar fulani a tarayyar Najeriya wadda aka fi sani da Miyetti Allah Kautal H0re Fulani ta yi hasashen cewa kasar Najeriya za ta shiga wani yanayi na rashin tabbas idan har Atiku Abubakar ya lashe zaben 2019.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban Sakataren ta na kasa, Saleh Alhassan ya fitar kuma jaridar Punch ta wallafa daga garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Akwai matsala idan Atiku ya zama shugaban kasar Najeriya - inji kungiyar fulani

Akwai matsala idan Atiku ya zama shugaban kasar Najeriya - inji kungiyar fulani
Source: Facebook

KU KARANTA: Dangote yayi abun azo a gani a jihar Zamfara

Sanarwar manema labaran ta cigaba da cewa suna Allah-wadai da kalaman dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da yayi inda yace wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ba cikakken bafullatani bane.

Inji Saleh Alhassan, wannan ba gaskiya bane domin kuwa ko a siffar jiki ma, Shugaba Buhari din yafi Atiku kama da fulani kuma iya yaren fulatanci ba shine ke tabbatar da zaman mutum kabilar ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a 'yan kwanakin nan jaridu da dama sun ruwaito kungiyar ta Miyetti Allah Kautal H0re Fulani ta goyi bayan tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel