Rashin lafiya: Shugaba Buhari garau yake yanzu – DG APC Ekiti

Rashin lafiya: Shugaba Buhari garau yake yanzu – DG APC Ekiti

Yayin da ake ta surutu a game da lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC a zaben 2019 tayi wuf ta karyata cewa shugaban kasa bai cikin koshin lafiya.

Rashin lafiya: Shugaba Buhari garau yake yanzu – DG APC Ekiti

APC tana ganin cewa shugaban kasa Buhari garau yake
Source: Depositphotos

Kwamitin yakin tazarcen Buhari/Osinbajo da jihar Ekiti ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari yana cikin koshin lafiyar da zai yi kara yin shekaru 4 yana mulkin kasar nan. Shugaban wannan kwamiti ya bayyana wannan.

Darekta Janar na yakin neman zaben APC a yankin Ekiti ta tsakiya a zaben 2019, Dr Olusegun Osinkolu, da kuma mataimakin sa Taiwo Olatunbosun sun fadawa Duniya cewa Buhari yana da duk isasshiyar lafiyar da ake bukata.

lusegun Osinkolu da Taiwo Olatunbosun sun yi wannan magana ne a lokacin da su ka tara ‘yan jarida a cikin garin Ado Ekiti a karshen a Ranar Talata inda su kace maganar da ‘yan adawa su ke yi na cewa Buhari bai da lafiya, karya ne.

KU KARANTA: PDP ta fadawa Buhari ya gurfanar da Oshiomhole da Amaechi

Osinkolu da abokin aikin na sa Olatunbosun sun bayyana cewa yanzu haka shugaba Buhari yana yawon kamfe gari zuwa gari don haka babu yadda za a ce kuma bai da koshin lafiya. Buhari dai ya je Bauchi, Yobe, Kogi da sauran su.

Kwamitin yakin neman zaben na APC tayi tir da maganar da Olusegun Obasanjo yayi inda yace Buhari bai da cikakken lafiya, duk da cewa shi ba Likita bane. Olatunbosun ya cika baki yana mai cewa Buhari ya ci zabe a jihar Ekiti ya gama.

Wasu manyan ‘yan adawa su na ganin cewa Buhari bai da karfin da zai iya cigaba da mulkin kasar nan bayan 2019 don haka shugaban kasar ya hakura ya huta. Sai dai APC tana ganin cewa Buhari garau yake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel