Na-Allah-basu-karewa: Aliko Dangote yayi wani abun azo-a-gani a jihar Zamfara

Na-Allah-basu-karewa: Aliko Dangote yayi wani abun azo-a-gani a jihar Zamfara

Shahararren dan kasuwarnan, wato Aliko Dangote a jiya Litinin ya tallafawa da ‘yan gudun hijirar da rikici da rashin zaman lafiyar jihar Zamfara da kayayyakin abinci da kayan masarufi na miliyoyin Nairori fisabilillah.

Tallafin wanda ya gudana a karkashin gidauniyyarsa ta ‘Aliko Dangote Foundation’, an kiyasta cewa; akalla ‘yan gudun hijira dubu 30 ne suka amfana daga wannan tallafin.

Na-Allah-basu-karewa: Aliko Dangote yayi wani abun azo-a-gani a jihar Zamfara

Na-Allah-basu-karewa: Aliko Dangote yayi wani abun azo-a-gani a jihar Zamfara
Source: UGC

KU KARANTA: Kungiyar Atiku ta karrama Sheikh Gumi

Anthony Chiejina, wanda shi ne shugaban sadarwa ya bayyana cewa; hare-haren da ake kaiwa a jihar Zamfara, yasa dubban al’umma sun rasa matsugunansu a jihar.

Inda a halin yanzu wadansu da yawa suna samun mafaka a karamar hukumar Maradun dake jihar Zamfarar. Ya ci gaba da cewa; a hukumance ma an bayyana cewa; akalla mutane dubu 3000 ne suka rasa rayukansu.

A yayin da dama sama da dubu 100 kuma suka bar gidajensu, inda kuma mutane dubu 30 ke gudun hijira a karamar hukumar Maradun. Inda kuma aka sace fiye da mutane 500.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel