Kewaye kake da barayi, ka daina ce mana munyi satar kudin gwamnati - PDP ga Buhari

Kewaye kake da barayi, ka daina ce mana munyi satar kudin gwamnati - PDP ga Buhari

- Jam'iyyar PDP ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da ya hukunta na kusa dashi da ake zargi da rashawa

- Jam'iyyar ta zargi shugaban da bawa shuwagabannin APC kariya

- Tayi kira ga shugaban da ya hukunta Babachir Lawal da Ayodele Oke

Kewaye kake da barayi, ka daina ce mana munyi satar kudin gwamnati - PDP ga Buhari

Kewaye kake da barayi, ka daina ce mana munyi satar kudin gwamnati - PDP ga Buhari
Source: Depositphotos

Jam'iyyar PDP ta kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hukunta shuwagabannin jam'iyyar APC da ake zargi da rashawa.

Ta bukaci shugaban kasar da ya sha gaban sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal da tsohon darakta janar na NIA da kuma hukunta sauran shuwagabannin jam'iyyar shi da aka kama da laifin rashawa.

Jam'iyyar ta mika wannan bukatar ne a ranar talata ta hannun daraktan yada labarai na yakin neman shugabanci kasa na PDP, Kola Ologbondiyan.

An zargi shugaban kasar da ba shuwagabannin jam'iyyar da ke kusa dashi kariya misalin Babachir Lawal da Ayodele Oke. Don haka PDP ta bukaci shugaba Buhari da ya gaggauta hukunta shuwagabannin APC da ake zargi da rashawa.

GA WANNAN: Siyasar 2019: Bayan Izala ta raba kan Musulmi a kan 'yan takara, ga abinda CAN ta tofa kan zaben

Jam'iyyar tayi kira ga shugaban da ya gagauta hukunta tsohon mataimaki na musamman ga uwargidanshi, Aisha Buhari, Mista Baba Inna, wanda aka kama a watan satumba na shekarar da ta gabata da zargin shi na karbar Naira biliyan 2.5 daga yan siyasa, yan kasuwa da mata a madadin uwargidan shugaban kasar.

"Shugaban kasa Buhari ya bayyana umarnin hukunta mutanen da ke kusa dashi dake da hannu dumu dumu a mallakar Naira tiriliayan 1.032 da ake zargin an same su ta rashawa ne daga kamfanin 9mobile da bankin Keystone," inji jam'iyyar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel