Wadanda su kayi garkuwa da surukin Marafa sun nemi a biya su N30m kudin fansa

Wadanda su kayi garkuwa da surukin Marafa sun nemi a biya su N30m kudin fansa

'Yan bindiga da suka kai farmaki a wasu garuruwa na jihar Zamfara sun nemi a biya su Naira Milyan 30 a matsayin kudin fansa kafin su saki Alhaji Ibrahim, mijin marigayiya Ade Marafa.

Ade Marafa yaya ce ga Sanata Kabiru Marafa mai wakiltan Zamfara ta Tsakiya wadda 'yan bindiga suka kashe ta.

'Yan bindigan sun kuma kone garin Ruwa Bore da ke karamar hukumar Gusau kurmus.

Sanata Marafa: Masu garkuwa sun nemi a biya su N30m kudin fansa

Sanata Marafa: Masu garkuwa sun nemi a biya su N30m kudin fansa
Source: Twitter

Wani mazaunin garin da ya yi magana da Sahara Reporters ya ce 'yan bindigan sun kira iyalan Alhaji Ibrahim inda suka bukaci a biya kudin kafin su sako shi.

DUBA WANNAN: EFCC: Shaida ya bayyana yadda Shekarau da wasu mutane 2 suka kasafta N950m

"Sun kira sun nemi a biya Naira Miliyan 30," inji shi.

Ya ce 'yan bindigan sun zo da niyyar sace yayan Marafa ne amma sai taki amincewa su tafi da ita.

"Lokacin da suka iso, sunyi kokarin tafiya da ita amma taki amincewa. Sai suka kashe ta sannan suka tafi da mijinta."

'Yan bindigan sun kai farmaki ne a garin a safiyar ranar Talata inda suka kashe mutane 14 sannan suka kone unguwanni biyu, Tungar Takoka da Tudun Wadae Maijatau.

Mazauna garin sun yi hijira zuwa garin Mada da sauran garuruwan da ke makwabtaka da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel