Atiku Abubakar ya zabo wata jarumar fim domin ta tayashi yakin neman zaben 2019

Atiku Abubakar ya zabo wata jarumar fim domin ta tayashi yakin neman zaben 2019

Tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zabo wata kyakkyawar jarumar fina finan turanci na Najeriya, da akafi sani da suna Nollywood, Regina Daniels domin ta tayashi yakin neman zabe.

Legit.ng ta ruwaito Atiku ya nada wannan jaruma ce mukamin jami’a mai kula da matasan Nollywood gaba daya, ta yadda zata karkato masa ra’ayin matasan Nollywood da nufin su bashi goyon baya tare da tallatashi, har sai ya kai ga nasara a zaben shugaban kasa.

KU KARANTA: Jama’an jahar Yobe sun yi fitar farin dango wajen tarbar Buhari yayin da ya shiga Damaturu

Atiku Abubakar ya zabo wata jarumar fim domin ta tayashi yakin neman zaben 2019
Regina
Source: Instagram

Jarumar mai shekaru goma sha takwas a rayuwa ce ta sanar da wannan cigaba da ta samu a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda tace tana goyon bayan Atiku dari bisa dari, kuma zata bada duk gudunmuwar data dace don ganin ya samu nasara.

“Sunana Regina Daniels, ina alfahari da kasancewata yar Atiku dari bisa dari, na amince da mukamin daya nadani na mai kula da matasan Nollywood, zan yi aiki tukuru saboda Atiku mutum ne mutunta matasa, kuma yayi alkawarin zai baiwa matasa mukamin ministoci a gwamnatinsa.

“Najeriya na cikin mawuyacin hali, jama’a na fama da yunwa, lokaci yayi da zamu karkatar da akalar kasar zuwa tudun mun tsira, tun daga Bama har zuwa Bori, Aba zuwa Abuja, Kaura Namoda zuwa Kaduna, lokaci yayi da matasan Najeriya zasu hada kai dani wajen zaban Atiku/Obi a 2019 don kare rayuwarmu.” Inji ta.

Regina na daga cikin fitattun jaruman fina finan Nollywood da suka bayyana goyon bayansu ga tafiyar Atiku Abubakar a shafukan sadarwar zamani, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar masana’antar Kannywood da ta Nollywood ta rabu gida biyu tsakanin yan Atiku da yan Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel