Gwamnan Bauchi ya shigo da makamai saboda a murde zaben bana - Dogara

Gwamnan Bauchi ya shigo da makamai saboda a murde zaben bana - Dogara

Mun ji cewa Kakakin majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon Yakubu Dogara, ya bayyana shirin da gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar esq. yake yi na kawo tashin hankali a zaben da za ayi.

Gwamnan Bauchi ya shigo da makamai saboda a murde zaben bana - Dogara
Ana yunkurin shigo da makamai a Bauchi murde zabe inji Dogara
Source: UGC

Honarabul Yakubu Dogara yana zargin gwamnan Bauchi da kokarin shigo da makamai da za ayi amfani da su wajen murde zaben bana. Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da ‘yan siyasa su ka shirya a jihar Bauchi.

Kakakin majalisa, Dogara yace yana da hujjar cewa gwamnan na sa ya kawo manyan bindigogin da za su yi amfani wajen kawo hatsaniya a jihar Bauchi domin ganin APC ta cigaba da mulkin da karfi da yaji bayan zaben na 2019.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun fara tanadin makami domin zaben 2019

Yakubu Dogara yace gwamnan jihar yana kitsa wannan sharri ne saboda asalin sa bako ne ba ainihin mutumin Bauchi bane. Wannan ne ya sa shugaban majalisar ya hada kai da manyan ‘yan siyasa wajen ganin sun tika APC da kasa.

Rt. Hon. Dogara ya bada labarin yadda aka kama wani Matashi mai suna Ilela da makami wajen zabe kwanaki inda yace gwamnatin APC mai mulki ta gaza wajen kawo cigaba ta fuskar abubuwa more rayuwa da cigaba a Bauchi.

Dogara dai yace duk da haka ba su na fada da gwamna Abubakar saboda bare bane sai dai ganin yadda jihar Bauchi ta sukurkuce a hannun sa. Kakakin kasar yake cewa gwamnati mai ci tayi facaka da biliyoyin kudin kananan hukumomi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel