Kan ku ake ji: Babu abin da zai sa Buhari yayi muhawara da su Moghalu da Ezekwesili inji Sagay

Kan ku ake ji: Babu abin da zai sa Buhari yayi muhawara da su Moghalu da Ezekwesili inji Sagay

Farfesa Itse Sagay wanda shi ne shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara game da harkar rashin gaskiya, yayi magana game da batun muhawarar da aka shirya jiya.

Kan ku ake ji: Babu abin da zai sa Buhari yayi muhawara da su Moghalu da Ezekwesili inji Sagay
Muhawarar zabe bai da wani amfani wajen Buhari inji Sagay
Source: UGC

Muhammadu Buhari da Atiku duk sun ki halartar zaman da aka yi jiya tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa. Itse Sagay ya fito ya kare shugaban kasar inda ya nuna cewa muhawarar da ake shiryawan ba wani kayan gabas bace.

Sagay wanda babban masanin harkar shari’a ne yace babu inda dokar kasa tace sai shugaban kasa ya halarci muhawarar da aka shirya a lokacin zabe. Farfesan ya nuna cewa ayyukan yi sun yi wa shugaba Buhari yawa a halin yanzu.

KU KARANTA: Ban halarci muhuwara bane saboda al'amura sun yi mani yawa - Buhari

Farfesan yake cewa sauran ‘yan takarar ba su da abin yi ne don haka su ka halarci muhawarar da aka shirya. Sagay yace babu abin da kananan ‘yan takarar su ka sa gaba sai babatu da banbami wanda ba shi ne asalin aiki a kasa ba.

Itse Sagay wanda yana cikin masu ba Buhari shawara yayi wannan bayani ne lokacin da yayi hira da Jaridar The Sun Newspaper. Sagay yace bai ganin akwai wani tasiri don Buhari ya tsaya da wasu kananan ‘yan siyasa yana surutu.

A cewar Itse Sagay, sauran ‘yan takarar za su kara samun farin jini ne kurum idan su ka tsaya su na kunfar baki da shugaban kasa Buhari. Don haka ne Sagay din yake ganin gara Buhari ya ji da sabgar gaban sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Online view pixel